• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Matsalar da matan da su ka yi fim su ke fuskanta a gidan aure – Zuwaira Abdussalam

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 14, 2022
in Labarai
0
Hajiya Zuwaira Abdussalam

Hajiya Zuwaira Abdussalam

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHUWAR jarumar Kannywood, Hajiya Zuwaira Abdussalam, wadda aka fi sani da Zuwaira Juda, ta bayyana ɗaya daga cikin dalilan da ke sa auren matan da su ka yi fim ya ke mutuwa.

Zuwaira dai ta na ɗaya daga cikin jaruman da su ka daɗe ana damawa da su a harkar fim a da, amma kuma sai aka daina ganin ta na tsawon lokaci.

Sai dai yanzu kuma ana ganin ta a cikin shirin ‘Ɗaɗin Kowa’ na gidan talbijin na Arewa 24.

Mujallar Fim ta tuntuɓi jarumar kan doguwar ɓacewar da ta yi daga industiri. Sai ta ce: “To gaskiya ne an ɗauki lokaci mai tsawo ba a gani na, duk da cewar an san ni ina cikin jarumai mata na kusan farko a cikin harkar fim. Amma dai abin da zan faɗa shi ne na yi aure ne a shekarun baya, ina gidan miji na, shi ya sa ba a gani na. Don ka san mu mata duk wadda ta yi aure za ta zauna a gidan mijin ta ne saboda aure ba wasa ba ne.

“To amma a yanzu dalilin da ya sa aka fara gani na, musamman masu kallon shirin ‘Ɗaɗin Kowa’, a yanzu mun rabu da miji na ne. Ka san shi aure rai ne da shi, idan kwana ya ƙare sai an rabu .”

Dangin miji ne matsalar aure ga mata ‘yan fim, inji Zuwaira Abdussalam

Dangane da yadda zaman auren nata ya kasance ne Zuwaira ta yi bayanin wata babbar matsala da ‘yan fim mata su ke samu idan sun yi aure. Ta ce: “To, ka san mu ‘yan fim mata mu na samun matsaloli a zaman aure, domin sau da yawa mu kan samu matsala a wajen dangin miji. Sai ka ga duk da mu na zaman aure ne, amma su dangin miji su na yi mana kallon ‘yan fim, ba su na yi mana kallon matan aure ba. 

“Ka san dai abin da na ke nufi idan an ce yarinya ta na fim, kowa ya gane me na ke nufi! To wannan kallon ‘yan fim da ake yi mana, shi ya ke haifar mana da matsalar zaman aure.

“Amma dai ni a kai na na iya jure wannan matsalar, don haka ba ita ce ta raba ni da miji na ba; abin da ya raba ni da miji na wani abu ne daban wanda ya ke sirri na ne. Tsakani na kuma da miji na ne, wanda ba sai duniya ta ji ba.”

Da ta ke bayani kan bambancin harkar fim ta yanzu da ta da kuwa, sai tsohuwar jarumar ta ce, “A gaskiya, harkar fim ta yanzu ta bambanta da ta baya, domin a yanzu ka ga babu haɗin kai kuma ba a zumunci, kowa sai ka ga harkar gaban sa ya ke yi, ba kamar na baya ba da in abu ya samu ɗan fim to ya samu kowa a cikin harkar. 

“To gaskiya a yanzu na ga babu haɗin kai, kowa ta kan sa ya ke yi. Ka ga irin wannan bai dace da zaman tare ba.”

Zuwaira ta yi kira ga ‘yan fim, musamman mata, da su haɗa kan su kuma su yi zumunci a tsakanin su, domin ta haka ne za su riƙa maganin duk wata matsala da ta taso masu.

Loading

Tags: aureDaɗin Kowadangin mijijarumai mataZuwaira Abdussalam
Previous Post

Abin da ya sa na kafa ƙungiyar ‘Shura People’s Party’ – Nabraska

Next Post

2023: INEC ta yi watsi da sunayen waɗanda su ka yi rajistar zaɓe sau biyu – Okoye

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Farfesa Mahmood Yakubu

2023: INEC ta yi watsi da sunayen waɗanda su ka yi rajistar zaɓe sau biyu - Okoye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!