FURODUSA a Kannywood, Abubakar Bashir Abdulkareem, wanda aka fi sani da Maishadda, ya bayyana jin daɗi kan nasarorin da ya ke samu a masana’antar, shekara goma tun lokacin da ya shigo cikin ta.
Ya ce dogaro da Allah, jajircewa, dakakkiyar zuciya, aiki tuƙuru, kyakkyawar zuciya, riƙon gaskiya da amana da kuma yarda da cewar Allah (s.w.t.) zai isar wa bawa a inda bai isa ba, su na sawa a kai inda ba a tsammani a rayuwa.
Maishadda ya yi waɗannan kalaman ne a Instagram a yau Alhamis, bayan sun kammala ɗaukar wani aikin kwangila da kamfanin sadarwa na Glo ya ba shi.
Ya ce, “Na shigo masana’antar Kannywood a shekarar 2012 a matsayin ‘production manager’, sannan na fara shirya fim a shekarar 2014 da fim ɗin (darakta) Hafizu Bello mai suna ‘Bincike’. Sannan na ci awad ɗin AMVCA 2015 da fim ɗin ‘Bincike’ har ila yau.”
Ya ci gaba da cewa, “Yau a matsayi na na mai shirya finafinan Hausa da kuma ɗaukar nauyi, na samu dama na fara tallace-tallace, kuma bakin gwargwado an san fuskata.
“Kamfanin Globacom Limited sun kira ni, kuma na amsa kiran su. Kuma na kammala aiki na na yau a mutunce.
“Ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba a rayuwa ta. Allah ya taimaki masana’antar Kannywood, Allah ya yalwata mana arziƙin mu, ya ba mu zaman lafiya. Amin summa amin.
“Allah na gode, Allah na gode, Allah na gode. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (s.a.w).”
To, amin Maishadda.