‘YA’YAN Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Sokoto, ta zaɓi Malam Abdul Isma’il Musa a matsayin shugabannin su.
A yau Lahadi, 12 ga Disamba, 2022 aka gudanar da zaɓen sababbin shugabannin ƙungiyar a ɗakin taro na Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Kudu, a Jihar Sokoto.
Da farko an fara da tantance wakilai, waɗanda za su kaɗa ƙuri’a, daga misalin ƙarfe 10:00 na safe har zuwa ƙarfe 12:00 na rana.

Daga nan kuma, da misalin ƙarfe 12:30, aka fara kaɗa ƙuri’a. Bayan an kammala, sai aka faɗi sakamakon zaɓe.
Bayan an yi sallar azahar an dawo, sai aka rantsar da waɗanda su ka samu nasara.
An rantsar da su da misalin ƙarfe 2:30 na rana, sannan aka ba kowanne su satifiket, shaidar kama aiki.
Waɗanda su ka samu nasarar lashe zaɓen su ne: Abdul Isma’il Musa a matsayin Ciyaman; Shehu Ɗantuni Shagari, Mataimakin Ciyaman; Hajiya Halima Muhammad Baba, Sakatare; Bashiru Abdullahi Ejo, Mataimakin Sakatare, da Bala Ibrahim Kware, Ma’aji.
Sauran su ne Alhaji Sule Jibril, Sakataren Kuɗi; Murtala Hassan, Jami’in Hulɗa da Jama’a na 1; Yusuf S.Yaƙi, Jami’in Hulɗa da Jama’a na 2; Shafa’aru Sani, Jam’in Walwala; Abubakar Alhaji, Sakataren Tsare-tsare; Ɗahiru Muktar, Mai Binciken Kuɗi na 1, da Rabi’a Isa, Mai Binciken Kuɗi ta 2.
Da ya ke zantawa da mujallar Fim, wakilin uwar ƙungiyar ta ƙasa, kuma mai bincken kuɗi na biyu na ƙungiyar ta ƙasa, Malam Bello Achida, ya ce, “Ina godiya ga Allah da ya sa aka yi wannan zaɓen lafiya, kuma ina kira ga sababbin shugabanni da su yi wa mambobin su adalci, kuma su janyo waɗanda ba su yi nasara ba su tafi tare.”

