• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Adam A. Zango ga ‘yan fim: Ba mu da mafita sai mu gyara halayen mu marasa kyau

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 11, 2022
in Labarai
0
Adam A. Zango a cikin bidiyon da ya wallafa a soshiyal midiya

Adam A. Zango a cikin bidiyon da ya wallafa a soshiyal midiya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMI kuma mawaƙi a Kannywood, Adam A. Zango, ya yi wa ‘yan’uwan sa ‘yan fim matashiya kan wata magana da wani malami mai suna Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya yi a kan su a makon jiya.

Malamin ya saki wani gajeren bidiyo ne a soshiyal midiya inda ya kiran ‘yan fim ɗin Hausa da sunan marasa addini, kuma ya ce su na gudanar da haramtacciyar sana’a.

Maganar tasa ta harzuƙa wasu daga cikin ‘yan fim, inda har darakta Al-Amin Ciroma, da jarumi kuma mawaƙi Misbahu M. Ahmad su ka yi masa zazzafan martani.

A nasa bangaren, shi ma Adam A. Zango ya yi magana ne a wani bidiyo mai tsawon minti uku cif da ya wallafa a soshiyal midiya a yau Lahadi.

A bidiyon, wanda mujallar Fim ta kwafa, jarumin ya faɗa wa abokan sana’ar tasa cewa: “Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu ‘yan’uwa na ‘yan fim da kuma masoyan mu, ma’abota kallon finafinan mu da kuma sauraren waƙoƙin mu. Abubuwa sun cakuɗe game da wannan huɗuba da wannan malamin ya yi, ya harzuƙa ‘yan fim sosai, ran mu ya ɓaci. 

“To amma magana ta gaskiya shi ne Bahaushe ya ce idan ɓera na da sata, daddawa ma ta na da wari; idan za mu gyara, mu gyara. Maganar gaskiya kenan.”

Ya ci gaba da cewa: “Ni da kai da ku mun san inda ya ke da ɓuli ko in ce huji a cikin masana’antar mu, mun san inda ya ke a ɗinke. Ba yau aka fara yi mana wannan huɗubar a Jihar Kano ba, an yi mana wannan huɗubar da yawa, an yi addu’o’i a kan mu, an yi alƙunuti, kuma duk wannan abin da ake yi, yi ake yi wai don mu gyara. Amma ina! kowa ya na can ya na sabgar sa. Idan ka ga ‘yan fim sun haɗu cincirindo a wuri, to za a ba mu kuɗi ne ko kuma biki ne na ɗan’uwan mu ɗan fim, za mu zo mu caccashe a taka rawa, ko kuma mutuwa aka yi. Shi kan shi mutuwar idan ba babban jarumi ba ne ko babban furodusa ko babban darakta ya rasu, ba za ka ga cincirindon ‘yan fim ba, sai dai makusantar sa. Ka sani, na sani, kin sani!”

Zango ya ci gaba da cewa, “Aikin mu kullum shi ne mu je sitidiyo mu ɗauki hotuna, waɗanda su ka dace da wanda ba su dace ba, a zo a yi ta liƙawa a soshiyal midiya: wannan ya na ‘birthday’, waccan ta na ‘birthday’, duka a nan ake ganin mu. Ba za ka ji an ce ana Maulidi ga ‘yan fim ba, ana yin musabaƙa ko wa’azin ƙasa ko wani abu da ya shafi addini ko al’ada ba za ka gani ba. 

“Amma maganar gaskiya shi ne manyan mu su na iyakacin ƙoƙarin su wajen ɗinke ɓaraka in ta tunkaro mu. Idan su ka kira mitin domin a zauna a tattauna a kan wani abu da zai iya jawo mana tashin hankali ko kuma jawo mana matsala cikin al’umma, wallahi ba za ka ga ɗan fim ba, a’a, sai dai su ya su su zauna su yi mitin ɗin da wasu ƙalilan wanda su ka amsa kira. Amma ba za ka ga musamman matan mu ba za ka taɓa ganin su a wurin da aka ce taron ‘yan fim ba ne yau za a yi a wuri kaza domin a ja hankalin su a kan wani abu da mutanen gari ko in ce masu kallon mu su ke ganin ba daidai ba ne, a gyara. Ba za ka gan su ba, ko in ce ba za ka gan mu ba. 

“Amma dai kowa a cikin ‘yan fim su na da iyali, mata da ‘ya’ya, babban gida ko in ce malamai. Wasu ma iyayen su malamai ne sosai, wasu ma masu sarauta ne, da sauran su.

“To idan mu na tunanin cewa an san fuskar mu a duniya duk abin da mu ka yi za a kalla, to mummunan abin da mu ke aikatawa ma za a kalle shi a duniya – ko ka na so, ko ba ka so. Meye mafita? Mu gyara, faƙat.”

Loading

Tags: Adam A. ZangoAl-Amin CiromahalayyaIdris Abdul'aziz Dutsen TanshiKannywoodKanomartaniMisbahu M. Ahmadsoshiyal midiya
Previous Post

Yadda mota ta ta ƙone ƙurmus – daraktan Kannywood Aminu Bono

Next Post

Furodusan Kannywood Abdul Isma’il Musa ya zama shugaban MOPPAN ta Sokoto

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Ana rantsar da sababbin shugabannin

Furodusan Kannywood Abdul Isma'il Musa ya zama shugaban MOPPAN ta Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!