• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Marubuta sun kafa gidauniya don ɗawainiyar karatun yaran Auwal Ɗanborno

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 29, 2023
in Labarai
0
Marigayi Sufeto Auwal Garba Ɗanborno

Marigayi Sufeto Auwal Garba Ɗanborno

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MARUBUTA a Kano sun ta bayyana kafa wata gidauniya ta musamman don tallafa wa iyaye da iyalan marigayi Alhaji Auwal Garba Ɗanborno.

A sanarwar da su ka bayyana a soshiyal midiya a yau Alhamis, 29 ga Yuni, 2023, marubutan, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Umma Sulaiman ‘Yan’awaki (Aunty Baby), sun ce, “A madadin ‘yan’uwa marubuta da sauran abokan arzikin marigayi Auwal Garba Ɗanborno mu ke sanar da ku shiri na musamman domin tallafin zuri’ar ɗan’uwa, amini, musamman ta fuskar ilimin su.”

Mujallar Fim ta ruwaito labarin yadda marigayin, wanda sufeton ‘yan sanda ne kuma marubuci a Kano, ya rasu a haɗarin mota a hanyar sa ta zuwa gona a Jihar Jigawa. Ya bar matan aure biyu da iyayen sa uwa da uba da ‘ya’ya 10.

Mutuwar sa ta girgiza marubuta da sauran masoya sosai, musamman yadda ta zo ba zato ba tsammani.

Aunty Baby, wadda aminiyar marigayin ce, ta yi wani rubutu inda ta ba da sanarwar kafa gidauniyar, a ciki ta bayyana cewa babban burin Auwal Ɗanborno bai wuce ganin ya yi ƙoƙarin bai wa yaran sa tarbiyya da ilimi ba.

Ta ƙara da cewa, “Mafi girman ƙauna da karamci da masoyi zai samu daga masoyin sa bai wuce tallafar bayan sa a lokacin da ya yi ƙaura zuwa gidan gaskiya ba.

“Burin mu idan Allah ya sa mun iya haɗa abin da mu ke fata, to za mu yi ƙoƙari wurin ganin mun samar da wani abu da zai rinƙa samar da ‘yan kuɗaɗe da za mu rinƙa yin amfani da su wurin ɗawainiyar karatun yaran marigayin. Aiwatar da haka zai zama wata hanya ta tabbatar da  zumunci da girmama juna tsakanin mu da iyalan marigayin masoyin mu.”

Ta bayar da asusun banki guda biyu inda duk mai sha’awar agazawa zai saka kuɗi kamar haka:

1. Rahma Abdulmajid Sharif, 2080944326, UBA

2. Umma Suleiman, 3018191777, First Bank

Aunty Baby ta ce: “Za mu riƙa saka abin da ya wakana duk wanda ya tura tallafi domin samun natsuwa da kuma sanar da halin da ake ciki.

“Allah Ubangiji ya ba mu ikon sauke wannan nauyi, ya kuma jiƙan marigayi Alh. Auwal G. Ɗanborno, ya sa shi cikin aljannar Firdausi maɗaukakiya.”

Wakilin mu ya ruwaito cewa mutane da dama sun goyi bayan kafa wannan gidauniya kuma jim kaɗan da bayyana ta har wasu sun fara turawa da tasu gudunmawar.

Loading

Previous Post

Ta’aziyyar Auwalu Garba (24/12/1978-25/06/2023)

Next Post

Akwai daɗi da kuma ƙalubale a rubutun onlayin – Ummulkhairi Sani Panisau (Khairat Up)

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ummulkhairi Sani Panisau (Khairat Up)

Akwai daɗi da kuma ƙalubale a rubutun onlayin - Ummulkhairi Sani Panisau (Khairat Up)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!