MARUBUCIYA: Sa’adatu Isah Muhammad
KAMFANI: Nazzy Bookshop, Kano
SHEKARA: 2017
SHAFUKA: 144
FARASHI: N200
ISBN: Babu
Labari
Labarin wasu ’yan mata ne guda uku: Fadila, Farida, da kuma Fauziyya, wadanda kawancen su ya kullu ta sanadin kaddarar da ta hada su. Suna da uwargijiya, Hajiya Baraka, wadda a gidan ta Fadila da Farida su ke zaune.
Dukkan su sun yi alkawarin babu su babu soyayya da wani da namiji balle batun aure. A haka Allah Ya hada Fauziyya da Likita Ahmad inda su ka fara soyayya mai karfi a tsakanin su, wanda ya janyo su Fadila su ka fara yunkurin hallaka saurayin likitan.
Jigo
– Littafin na nuna illar tara abin duniya ta mummunar hanyar kawalci, kamar yadda Hajiya Baraka ta yi, a karshe ta kare a wulakance.
– Amfanin tuba ga mai zunubi. Kada mai sabo ya fidda rai daga samun rahamar Allah. Duba rayuwar Fauziyya a karshe.
Salo
Marubuciyar ta yi amfani da salo mai karsashi wajen isar da sakon ta. Duk da yake babu gwanintar harshe sosai, amma salon ya yi kyau, haka taurari da garuruwan labarin sun dace da yanayin sa. Sai sambarka.
Zubi Da Tsari
An zubo labarin ne ratata, ba tare da babi ko kanun labari ba. Tsarin labarin ya samu kulawa mai kyau, ta yadda yake rike mai karatu babu kosawa.
Ka’idojin Rubutu
An samu kurakurai wajen ka’idojin rubutu a littafin, musamman wajen saka alamomin rubutu ba a gurbin da su ka dace ba, da kuma wajen raba kalma da hade ta.
Ya kamata a kula kafin dab’i.
Kurakurai
1. Ba a amfani da alamar motsin rai (!) fiye da daya ko da sau nawa aka maimaita kalma. Duba shafi na 5 littafi na 1, wurin kiran Idi.
2. A bangon littafi na 1 da na 2 ba a lankwasa harafin ‘K’ ba, wanda (hakan) ya mayar da sunan littafin ‘Kaddarar Mu.’
3. Da wanne makulli Baraka ta kulle kawar ta Ruky da mijin ta Jamilu a daki kafin ta yi yunkurin kona su? Ko dai shirin nasu ya kai ya ba ta makullan dakin sa a lokaci kadan? Duba shafi na 38, littafi na 1.
4. Shafi na 39, littafi na 1: Hukuncin wata shida ya yi kadan ga Baraka, idan an yi la’akari tsarin dokar kasa, yunkurin kisan kai ya na debo wa mutum shekaru ne a gidan maza.
5. A shafi na 51, littafi na 1 Hajiya ta jefa wa Kwamishina hoto ta na yi masa barazana. A ina ta samu hoton, bayan kwanan ta daya a sel? Ko kuwa da ma yawo ta ke da shi?
6. Shafi na 118, littafi na 1: Fauziyya ta ce ba ta san makarantar da za a kai ta ba, amma sai ga shi ta ce daga jin sunan makarantar za a yi karatu. Da ma ana gane makaranta mai karatu daga suna?
7. Shafi na 39, littafi na 2: Lokacin da Fadila ta fito daga bandakin otal an ce sanye ta ke da tawul, amma har ta ja ‘yan’uwan ta su ka gudu ba a nuna inda ta canza kaya ba. Ko dai daga ita sai tawul ta gudu?
8. Shafi na 105, littafi na 2: An nuna Fadila ta fara shaye-shayen kayan maye kai-tsaye. Ya kamata a ce wani ne ya dora ta a hanya duk da damuwar da ta ke ciki.
9. A shafi na 39, littafi na 3: An nuna duka ‘yan matan uku matsalar su daya, amma a zahirin labarin Farida ce kawai ta gamu da yaudarar samari, sauran biyun su su ka ja wa kan su ko kuma kaddarar su ce ta zo a haka.
10. Bai kamata a ce lallai sai wani babban mai kudi ne ya auri Fauziyya ba; hakan zai sa wa makaranta (musamman ‘yan mata) dogon buri ko da sun yi kazamar rayuwa irin ta Fauziyya.
11. Tun da Fauziyya ta tuba bai kamata a ce ta ci gaba da amfani da kadara ko dukiyar da ta samu ta hanyar haram ba.
12. Babu lambar ISBN a littafin.
Duk da haka, littafin ya yi dadi da ma’ana. A gaida Sa’a bocal.
![]()







