A YAMMACIN Talata, 30 ga Afrilu, 2024 Allah ya azurta shahararren mawaƙi a Kannywood, Alhaji Sanusi Anu, da ‘ya mace.
Maiɗakin sa, Malama Nafisat, ta haihu da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a asibitin marigayi Manjo-Janar Abba Siri-siri da ke Filin Kanada, Sabuwar Unguwa, a Birnin Katsina.

Sanusi ya raɗa wa jaririyar suna A’ishatul Humaira.
Mawaƙin ya shaida wa mujallar Fim cewa yanzu ‘ya’yan sa 10.
Allah ya raya A’ishatul Humaira da sauran ‘ya’yan, ya kuma albarkaci rayuwar su, amin.

![]()







