• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumin Kannywood Ali Rabi’u Ali ya aurar da babbar ‘yar sa Saudat

by ABBA MUHAMMAD
July 15, 2024
in Ranar Murna
0
Jarumin Kannywood Ali Rabi’u Ali ya aurar da babbar ‘yar sa Saudat

Ali Rabi'u Ali (a tsakiya) tare da su El-Mustapha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN Kannywood kuma furodusa, Ali Rabi’u Ali (Daddy), ya aurar da babbar ‘yar sa, wato Saudat.

An ɗaura auren Saudat (Islam) da abin ƙaunar ta, Abdulbasid Salisu Abdullahi, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a jiya Lahadi a masallacin Khalifa Sheikh Ishaq Rabi’u da ke Goron Dutse, Birnin Kano, a kan sadaki N70,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alh

Ali Rabi’u Ali a tsakiyar dandazon mahalarta ɗaurin auren

aji Abba El-Mustapha, jarumi Alhassan Kwalle, mawaƙi Mudassir Ƙasim, Ahmad Bifa da Isma’il Khaleel Ja’en.

Kamar yadda mahaifin amaryar ya shaida wa mujallar Fim, ba su yi wani taro da ya haɗa maza da mata ba.

A ranar Alhamis an yi karatun Alƙur’ani tun daga safe har dare, a ranar Juma’a kuma an yi gaɗa, sannan a ranar Asabar kuma aka yi kamu.

Bayan an ɗaura auren, mahaifin amaryar da kan shi tare da mahaifiyar ta su ka ɗauke ta zuwa ɗakin mijin ta.

Ali Rabi’u ya yi wa ‘yan’uwa da abokan arziki godiya, inda ya ce, “Assalamu alaikum wa rahmatullah. Alhamdu lillah! Ina miƙa saƙon godiya da bangajiya bisa taya ni murnar auren ‘ya ta.

“Ina godiya ga waɗanda su ka halarci ɗaurin auren, da fatan kun koma gida lafiya. Haka waɗanda su ka turo da saƙo da waɗanda su ka yi addu’ar fatan alkhairi.

Ali Daddy (a hagu) tare abokan sa

“Na gode ƙwarai. Allah ya saka da alkhairi ga waɗanda su ka bani gudunmawa ta lafiyar su ko addu’a ko kuɗi, Allah ya sa a mizani, Allah ya bar zumunci. Na gode ƙwarai. Amarya da mahaifiyar ta na ƙara yi muku godiya.”

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

Loading

Tags: Ali Rabi'u Aliɗaurin aure
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya karɓi baƙuncin ‘yan jaridar da aka sace

Next Post

Nijeriya da UAE sun cimma yarjejeniya kan maido da ba ‘yan Nijeriya biza

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Nijeriya da UAE sun cimma yarjejeniya kan maido da ba ‘yan Nijeriya biza

Nijeriya da UAE sun cimma yarjejeniya kan maido da ba 'yan Nijeriya biza

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!