MANAJIN Daraktan Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, ya buɗe reshen kamfanin kayan shaye-shaye na kamfanin ‘Rufaida Drinks’ a Kano.
Ali ya ba da sanarwar buɗe sabon reshen ne a shafukan sa na soshiyal midiya, inda ya ce, “A ƙoƙarin mu na kawo dukkan samfuran mu kusa da ku, ‘FKD Rufaida Drinks’ ta ƙaddamar da wani sabon reshe a Magaji Rumfa da ke kan Titin Lafiya, Nasarawa GRA, Kano.”
An buɗe shagon ne tare da haɗa sunan kamfanin Ali, wato FKD, da sunan kamfanin Rufaida, inda ya zama ‘FKD Rufaida Drinks’.
Wannan ya tabbatar da cewa shagon na Ali Nuhu ne, ba kamar yadda aka saba ganin sunan kamfanin na Rufaida ba.
Ali Nuhu ya kasance ɗaya daga cikin masu tallata kayayyakin kamfanin ‘Rufaidah Drinks’. Kusan ana iya cewa shi ne a sahun gaba.

Duk da cewa Ali Nuhu ya kasance jarumi, darakta, marubuci, furodusa, sannan a yanzu kuma ma’aikacin gwamnati, amma kuma yana da wasu sana’o’in a gefe.
Ya na da shagon kayayyakin sawa na zamani, ƙananan kaya, wanda ake kira da ‘Don Ali Collection’, ya na kiwon kaji, sannan ga shi yanzu ya ƙara da shagon kayan maƙulashe.
Bugu da ƙari, shi ne jarumin da ya fi kowane jarumi yawan samun tallace-tallace na kamfanoni daban-daban, irin su kamfanin waya na ‘Samsung’, kamfanin sadarwa na ‘Glo’, kamfanin ‘Omo’, kamfanin ‘Herpic’, kamfanin ‘Yale’, da sauran su.
Sannan Ali bai tsaya ga kan shi kaɗai ba, ya kan samar wa sauran jarumai ire-iren waɗannan tallace-tallacen.
A ɓangaren tallar kamfanin ‘Rufaida Drinks’ kuwa, har wasu na tunanin kamfanin sa ne, saboda yawan tallar da ya ke yi masu.
Da mujallar Fim ta yi tambaya kan yadda Ali Nuhu yake gudanar da harkar kasuwanci bayan dokar gwamnati ta hana ma’aikatan ta yin harkar kasuwanci in ban da noma kaɗai, sai wata majiya ta kusa da jarumin ta ce, “Ai yanzu ba shi ke jan ragamar FKD da sauran kasuwancin sa ba tun bayan naɗa shi muƙamin shugaban NFC da aka yi. Ya naɗa wani yaron sa, Ali Bikon, a matsayin MD/CEO na kamfanin.
“Sannan Don Ali Collections kuma, wani yaron sa, Kabiru, aka buɗe wa.”
![]()







