ALLAH ya yi wa mahaifin mawaƙiya kuma jaruma a Kannywood, Ummi Abdullahi Adamu Birnin Yero, wadda aka fi sani da Ummi B.Y., rasuwa.
Alhaji Abdullahi ya rasu ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a jiya Asabar, 18 ga Janairu, 2025 a asibitin Barau Dikko Teaching Hospital (Nursing Home) da ke cikin garin Kaduna bayan ya sha fama da jinya na tsawon wata biyar.
Dattijon mai kimanin shekara 70 a duniya ya rasu ya bar matan sa biyu da ‘ya’ya 15. Ummi ita ce ‘yar sa ta fari.

An yi jana’izar a yau Lahadi da misalin ƙarfe 9:00 na safe a gidan sa da ke garin Birnin Yero, Jihar Kaduna.
Allah ya jiƙan sa da rahama, ya kuma albarkaci dukkan abin da ya bari.

![]()







