• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

by ALI KANO
June 23, 2025
in Labarai
0
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

Rahama Sadau da mahaifin ta, marigayi Alhaji Ibrahim

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MANYAN ƙungiyoyin harkar fim a Kannywood, wato Kannywood Film Industry Guilds and Associations of Nigeria (KAFIGAN) da kuma Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), sun miƙa saƙon ta’aziyyar su ga jaruma Rahama Sadau a kan rasuwar mahaifin ta.

Mahaifin nata, Alhaji Ibrahim Sadau, ya rasu ne a Kaduna jiya da asuba sakamakon gajeren rashin lafiya.

Ɗimbin ‘yan fim sun je har gida sun yi iyalan mamacin gaisuwa, yayin da wasu kuma suka kira ta waya suka yi gaisuwa.

Ƙungiyar KAFIGAN ta tura nata sakon ne ta hanyar wasiƙa inda ta ce tana miƙa saƙon ne “har cikin zuci”.

A takardar, wadda Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar, Al‑Amin Ciroma, an ambato cewa Shugaban kwamitin Amintattun KAFIGAN, Alhaji Isma’il Na’Abba Afakallah, ya miƙa ta’aziyyar ƙungiyar ga Rahama da dukkan iyalan marigayin.

Ƙungiyar ta ce: “Rahama Sadau ba kawai ta yi fice a matsayin jarumar Kannywood da Nollywood ba ne, har ma ta sama wa kan ta gurbi ba musamman a masana’antar industiri a Afrika.
“An ji matuƙar zafin wannan rashi na mahaifin ta a cikin KAFIGAN da ƙasa baki ɗaya and beyond.”

Afakallah ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin. Ya ce: “Allah Ta’ala ya saka wa Alhaji Ibrahim Sadau da
Aljannatul Firdaus, kuma ya ba iyalin sa jimirin jure wannan babban rashi.”

A nata ɓangaren, MOPPAN ta rubuta wa Rahama Sadau takarda da sa-hannun Jami’in Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Malam Ibrahim Amarawa, a madadin shugaban ta.

MOPPAN ta ce wa jarumar: “A cikin matuƙar baƙin ciki tare da nauyin zuciya muke miƙa ta’aziyyar mu a gare ki da iyalan ku a kan rasuwar baban ku abin ƙaunar ku. Muna addu’ar Allah (SWT) ya yi masa sakayya da Jannatul Firdaus kuma ya lulluɓe shi da rahamar sa har abada.

“Mahaifin ku ya yi kyakkyawar rayuwa mai alƙibla, ya bar baya da kyakkyawan tunani, da kyautatawa da ƙarfin hali waɗanda za su ci gaba da zama a zukatan duk wanda ya san shi.

“Gudunmawar sa ga iyalan sa da al’umma da addini shaidu ne ga kyakkyawar halayyar sa.

“A yayin da kuke jimamin rasuwar sa, muna addu’ar Allah ya ba ku haƙurin jure wannan babban rashi.

“A wannan lokaci na baƙin ciki, ku tuna cewar Allah yana tare da masu haƙuri. Muna fatan tunowa da shi da soyayyar shi za su kasance jagora a gare ku tare da ba ku kwanciyar hankali. Muna tare da ku kuma muna jin zafin rashin da kuka yi.

“Allah ya gafarta masa dukkan kurakuran da, ya karɓi ayyukan sa na alheri, ya his jiƙan sa har abada. Ameen.”

Loading

Tags: Alhaji Ibrahim SadauKAFIGANMOPPANRahama Sadaurasuwar mahaifita'aziyya
Previous Post

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

Related Posts

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Kotu a Kano ta ɗaure ɗan TikTok Abubakar Kilina shekara ɗaya ko zaɓin tara
Labarai

Kotu a Kano ta ɗaure ɗan TikTok Abubakar Kilina shekara ɗaya ko zaɓin tara

June 19, 2025
Next Post

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!