A DAREN Lahadin da ta gabata Allah ya ɗauki ran Isma’il, babban ɗan mawaƙi kuma tsohon Kansilan Mazaɓar Gani da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, Tukur Musa Ɗankulla (TK).
Ya rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare a Asibitin Horeb da ke Titin Constitution, Kaduna, bayan gajeruwar jinya.

An yi jana’izar sa a jiya Litinin a ƙofar gidan kakan sa, marigayi Alhaji Musa Ɗankulla, da ke Titin Zariya, da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Yaron, mai kimanin shekara biyar da sati ɗaya, ya rasu ya bar mahaifin sa, mahaifiyar sa da ƙanan sa.
Gobe Laraba za a yi addu’ar uku a masallacin ƙofar gidan marigayi Alhaji Musa Ɗankulla da ke Titin Zariya da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar sun haɗa da tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Malam Sama’ila Sulaiman; Kakakin Majalisar Jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Ɗahiru Liman; ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin Gwari, Honorabul Bashir Zubairu; Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, Honorabul Ibrahim Beckham, da kansilolin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa guda takwas daga cikin su.
Allah ya jiƙan Isma’il, amin.
![]()







