SHUGABAN Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, bayyana ƙudirin hukumar sa na gina Cibiyar Fasahar Shirya Finafinai a Gombe.
Ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan ya kai ziyarar aiki ga gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, a gidan gwamnatin Jihar a yau.
Bayan ziyarar, Ali Nuhu ya miƙa godiyar sa ga gwamnan, inda ya ce, “Ina miƙa godiya ta musamman ga mai girma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa kyakkyawar tarba da na samu a yayin ziyara ta a yau.”
Daga nan ya bayyana ainihin dalilin ziyarar tasa, ya ce, “Tattaunawar mu ta kasance mai cike da ma’ana da hangen nesa. Mun tattauna kan Cibiyar Fasahar Shirya Finafinai (Cinematography Centre), wadda Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation) za ta kafa a Gombe, cibiyar da za ta zama ginshikin ƙirƙira, fasaha da ƙwararrun ayyukan shirya finafinai a wannan yanki.
“Haka kuma mun yi nazari kan damar koyon sana’o’i da shirye-shiryen horar da matasa, domin ba su ilimi da kayan aiki da za su taimaka musu su yi fice a harkar ƙirƙira.
“Bugu da ƙari, mun tattauna kan haɗin gwiwa tsakanin Makarantar Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Institute) da Jami’ar Jihar Gombe domin ƙarfafa alaƙar ilimi da masana’antu tare da samar wa ɗalibai da hanyoyin shiga fagen finafinai da kafofin watsa labarai.”
A ƙarshe, shugaban hukumar ya ce, “Ina da yaƙinin cewa waɗannan shirye-shirye ba za su tsaya ga haɓaka tattalin arzikin ƙirƙira a Gombe kaɗai ba, har ma za su buɗe sabon babi na ci gaba ga masana’antar finafinai ta Nijeriya gaba ɗaya.”
![]()







