A SAFIYAR yau aka fara Bikin Finafinai Na Duniya Na Kaduna, wato a Turance ‘Kaduna International Film Festival’, karo na uku.
Bikin, wanda ake shirya shi duk shekara, an fara shi ne a 2018.
An fara bikin daga yau Talata, 25 ga Agusta, 2020, kuma za a yi sho zuwa ranar Asabar mai zuwa, wato tsawon kwana biyar kenan.
A baya an saba shirya bikin ne a ɗakunan taro, amma a wannan karon abin ya zo da sabon salo, za a yi shi ne ta hanyar intanet.
Za a yi amfani da manhajar ZOOM wadda ake amfani da ita wajen shirya tarurrika a wannan zamani, ba sai an haɗu ido da ido ba.
Yadda ake amfani da wannan manhajar shi ne, za ka sauke manhajar a wayar ka, sannan ka yi rijista. Bayan ka yi rijista, akwai ID da password da ake ƙirƙira na wannan haɗuwar da za a yi don a tattauna.
Manhaja ce ta bidiyo wadda duk wanda ya shiga tsarin zai kalla tare da sauraron waɗanda ake tattaunawa da su.
An shirya amfani da manhajar don shirya bikin finafinan na Kaduna ne a zamanance sakamakon annobar korona bairos (Covid-19) da ta addabi duniya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an ƙirƙiri bikin domin ‘yan fim na Arewa, wato Kannywood, to amma ƙalilan ne su ka ɗauki bikin da muhimmanci, domin ko a wannan karon kusan dukkan waɗanda za su gabatar da tattaunawa a taron ba ‘yan Kannywood ɗin ba ne.
Kashim Audu Israel, wanda shi ne madugu uban tafiya na wannan biki, kuma shi ne wanda ya ƙirƙiri bikin, ya yi ƙoƙari wurin ganin ya ci gaba da shirya bikin. Shi ya sa a bana ma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya yi dukkan mai yiwuwa don tabbatar da an gudanar da bikin.
Ga yadda jadawalin bikin ya ke:
Talata, 25 ga Agusta, 2020 – Rana ta 1
PANEL DISCUSSION
“Encouraging Creativity/Skill in Post COVID-19 Era”
(12:00PM-2:00PM)
-Halima Gumel
-Mary Uche
-Fatima Umar Muhammad
-Ruƙayya Manga (Moderator)
-Francis Onwochei
-Amb Tokunbo
“Decency and Morals in the Entertainment Industry”
(3:00PM-5:00PM)
-Rukky Bent
-Rachel Bakam
-Hadiza Muhammad
-Emeka Ossai
-Sunday Awoji
-Leah Katung (ModErator)
Ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2020 – Rana ta 2
PANEL DISCUSSIONS
“Good Marketing Strategies and Movie Funding in the Film Industry”
(9:00AM-11:00AM)
-Tokumbo Jaboro
-Jebo Bature
-Kunle Afolayan
-Rachael Bakom
-Myke Parish
-Swat (Moderator)
“The Positive and Negative Impact of Entertainment on the Girl Child, Youth and Women as We Encourage Creativity in a Post COVID-19 Era”
(11:00AM-1:00PM)
-Zack Orji
-Audu Maikori
-Ali Baba
-Dr. Betta Edu (Commissioner for Health, Cross River State)
-Abdullahi Ajiyo (Moderator)
-Funky Malam
“The Role of Entertainment in Promoting Harmony and Peace Development in the Society”
(3:00PM-5:00PM)
-DCP Frank Mba (Nigerian Police PRO)
-DCP Abba Kyari (IRT)
-Mama Ajasko
-Fr Chimaobi Ohoji
-Becky Madojemu (Maderator)
-Alex Usifa
-Dr. A.S. Bello
“Have Film Guilds and Associations Helped the Movie/Entertainment Industry?”
(6:00PM-8:00PM)
-Chinyere Nwabueze
-Wassh Waziri Hong
-Emmanuel Eyaba
-Lancelot Imasuen
-Robert Peters
-Ruƙayya Manga (Moderator)
Alhamis, 27 ga Agusta, 2020 – Rana ta 3
MASTER CLASS
Screen Acting (Zack Orji/Tony Akposheri)
(9:00AM-11:00AM)
DIRECTING MASTER CLASS
(Fred Amata, Ugezu J. Ugezu)
(12:00PM-2:00PM)
VISUAL TOURISM
ON TURUNKU, KADUNA STATE
Saleh Bala Saleh (Tour Guide)
(3:00PM-4:00PM)
PANEL DISCUSSIONS
“How Film Censorship Has Impacted the Movie Industry and the Role it Plays in Regulating What We Watch”
(6:00PM-8:00PM)
-Alhaji Adebayo Thomas (Executive Director NFVCB)
-Fred Amata
-Yemi Blaq
-Becky Madojemu (Moderator)
-Ibrahim Daddy
Juma’a, 28 ga Agusta, 2020 – Rana ta 4
VISUAL TOURISM
ON SOUTHERN KADUNA STATE
Sale Bala Sale (Tour Guide)
(9:00AM-10:00AM)
PANEL DISCUSSIONS
“Sustaining Our Cultural Content and Its Moral in Our Present Society; Has Film Promoted Our Culture?”
-Laide Bakare
-Bukky Campbell (Moderator)
-Alex Eyengbo
-Fatima Abbas Muhammad
-Tania Nwosu
-Dr. Shu’aibu Hussaini Phd
“The Role of Media in Our Modern Day Entertainment”
(6:00PM-8:00PM)
-Amina Atairu (Moderator)
-Katung Aduwak
-Ronke Oshadi
-John Coster
-Lucy Ameh
-Robby Bray
-Kiki Omeili
-Prof. Ayodele Joseph
Asabar, 29 ga Agusta, 2020 – Rana ta 5
PANEL DISCUSSIONS
“Humanitarian Heart and Its Impact for Humanity; Has Entertainment Any Role to Play?”
(9:00AM-11:00)
-Hajiya Haneefa Gane
-Zack Orji
-Tony Akpasheri
-Ugezu J. Ugezu
-Kantiyak Kanty Joel
-Akume Akume
-Abdullahi Ajiya (Moderator)
NORTHERN FILM MAKERS ROUND TABLE DISCUSSION
“Promoting Hermony Among Each Other and Sustainning Film Content”
(2:00PM-4:00PM)
-Hassan Giggs
-Rabi’u Rikadawa
-Asabe Madaki
-Ado Ahmad Gidan Dabino
-Nura MC
-Wassh Waziri Hong
-Rukayya Manga (Moderator)
CLOSING CEREMONY
ZOOM
(6:00PM)
-Performance
-Award Presentation
-Closing Prayer
-Closing Remark
-Closing Speech
Zainab Ahmad (Festival Director)
![]()






