• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Muna da hurumi kan muƙabalar mawaƙa – Hukumar Tace Finafinai

by MUKHTAR YAKUBU
September 21, 2025
in Labarai
0
Muna da hurumi kan muƙabalar mawaƙa – Hukumar Tace Finafinai

Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab'i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana cewa tana da ikon sa ido kan waƙoƙi da tarurrukan sha’irai a jihar.

Ta faɗi haka ne a cikin martanin da ta yi wa wani lauya a Kano mai suna Abba Hikima, wanda ya yi tsokaci game da ikon doka da hukumar take da shi kan sha’irai.

Kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito, lauyan ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin doka wajen saka baki a muhawarar da ke tsakanin wasu sha’irai biyu, wato Shehi Mai Tajul’izzi da Usman Maidubun Isa.

Sai dai hukumar, a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Satumba, 2025, wadda Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya sanya wa hannu, hukumar ta bayyana cewa wannan matsayi da Hikima ya ɗauka ba daidai ba ne kuma yana nuna kuskuren fahimta kan dokokin da suka kafa hukumar.

Hukumar ta ce, “Dukkan su Shehi Mai Tajul’izzi da Usman Maidubun Isa sha’irai ne da doka ta saka su a ƙarƙashin kulawa da duba aikace-aikacen su gare mu.”

Ta ce asalin abin da ya haifar da muhawarar da ta shiga tsakanin su ta samo asali ne daga kalaman waƙoƙin su, wanda hakan ya sanya lamarin cikin ikon hukumar bisa tsarin dokar ta.

A cewar ta, dokar kafa hukumar ta  bai wa hukumar ikon da ya haɗa da yin rajista da bayar da lasisi ga sha’irai; kula da abin da suke fitarwa (wato waƙoƙin su) da sa ido kan ayyukan su a bainar jama’a, wato yayin majalisi; tabbatar da bin doka da oda, ciki har da bincike, hukunta masu karya doka, ko dakatar da lasisin su idan ya zama dole.

“Saboda haka, hukumar tana da cikakken ikon doka wajen saka baki a irin wannan lamari, don kare zaman lafiya, tarbiyya da martabar ɓangaren masu yabon Manzon Allah (S.A.W.),” inji jami’in.

Ya ƙara da cewa, “Muna girmama ra’ayoyin masana a ɓangaren shari’a, tare da jan hankalin su kan cewa irin wannan kuskuren fassara daga masu ilmin doka, musamman waɗanda suka san tsarin doka irin shi Abba Hikima, na iya rage darajar hukumomin gwamnati.”

Hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da yin aiki cikin lumana da bin dokar hukumar kamar yadda ya kamata.

Hakan dai ya biyo bayan wani zama ne da ta kira mawaƙan biyu kan taron muƙabalar da suka yi a tsakanin su inda aka tashi baram-baram da neman tayar da hayaniya.

Shehi Tajul izzi ya je da lauyan sa, Abba Hikima, yayin da Usman Mai Dubun Isa bai samu zuwa ba, sai wakilci ya tura.

Bayan zaman ne Abba Hikima ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin gayyatar mawaƙan a kan muƙabalar da suka yi.

Loading

Previous Post

Wata ‘jami’a’ ta ba Rarara ‘digirin girmamawa’ na dakta

Next Post

An fitar da ƙa’idojin gasar Ranar Marubuta ta Duniya 2026

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
An fitar da ƙa’idojin gasar Ranar Marubuta ta Duniya 2026

An fitar da ƙa'idojin gasar Ranar Marubuta ta Duniya 2026

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!