MASHIRYA taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya wanda za a yi a Jihar Jigawa a ƙarshen Disamba sun bada sanarwar rufe rajista ga masu buƙatar halartar taron.
Hakan ya biyo bayan cikar wa’adin da aka ɗauka na karɓar sunayen mutanen da za su halarci taron.
A ƙididdigar da shugabannin taron suka yi, an gano cewa ya zuwa jiya Alhamis an samu waɗanda suka yi rajista mutum
178.
Za a yi taron ne daga ranar 31 ga Disamba, 2025 zuwa ranar 1 ga Janairu, 2026 a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Duk wanda ya yi rajista, an yi masa fostar musamman ta taron da hoton sa, wadda ake yaɗawa a soshiyal midiya domin tallata taron.
A fostar akwai bayanin taron tare da asusun banki na Hajiya Umma Suleiman ‘Yan’awaki don biyan kuɗin rajistar da kuma yawan kuɗin.
A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na taron na bana, Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka), ya fitar da misalin ƙarfe 12 na daren Alhamis ɗin, ya bada sanarwar cewa, “Haƙiƙa marubuta sun nuna cewar su dangin juna ne, an yi kira sun amsa, sun nuna kishin rubutu da marubuta.
“Muna amfani da wannan damar mu yaba wa dukkanin waɗanda suka yi rajista, mun tabbatar sun yi ne domin kishi.
“Waɗanda ba su samu damar yi ba, muna musu fatan alheri, mun san wasu uzurori ne suka hana, kuma tabbas suna tare da kishin rubutu.
“Muna so mu haɗu mu dukkan mu don Allah, mu yi addu’o’i da nufin Allah ya sa mu yi taron nan lafiya, mu gama lafiya cikin nasara. Allah ya yi mana jagora, amin.”

![]()







