GWAMNATIN Jihar Kaduna ta sha alwashin za ta yi aiki tuƙuru tare da haɗin gwiwa da ƙungiyar Kannywood Film Industry Guilds and Associations of Nigeria (KAFIGAN) domin dawo da martabar harkar finafinan Hausa a Nijeriya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Ahmed Maiyaƙi, shi ne ya bayyana haka a wurin taron ƙaddamar da ƙungiyar a daren jiya Juma’a a Kaduna.
Ita dai KAFIGAN, sabuwar ƙungiyar haɗaka ce ‘yan fim ɗin Kannywood baki ɗaya wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin masu gudanar da harkar fim a ɓangarori daban-daban.
An gudanar da taron ƙaddamarwar a otal ɗin Epitome Hotel and Suites da ke unguwar Barnawa, Kaduna.
Kamar yadda aka tsara tun da farko, za a fara taron ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, amma an ɗan samu jinkiri, wanda ya sa sai ƙarfe 9:00 aka fara.
Bayan isowar dukkan membobi, ‘yan Kwamitin Amintattu, shugabannin ƙungiyar na ƙasa da na jihohi, manyan baƙi da babban baƙo na musamman, sai aka buga taken Nijeriya, aka buɗe taro da addu’a.
An gudanar da addu’a ta musamman ga Jami’in Yaɗa Labarai na ƙungiyar a reshen Jihar Kaduna, Malam Adamu Ibrahim Kabala, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Litinin da ta gabata. Malam Yahaya Adamu (Skito) shi ne ya jagoranci gudanar da addu’o’in.
Daga nan aka gabatar da baƙi mahalarta da kuma baƙi na musamman. Sai aka saurari jawabin maraba daga bakin shugaban Kwamitin Amintattu, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu), wanda ya yabi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a bisa irin yadda ya jajirce wajen ganin ya kawo cigaba ga jihar.

Haka kuma ya yi wa mahalarta taron maraba da zuwa, sannan ya yi addu’ar Allah ya sa a yi taro lafiya, a watse lafiya.
Bayan ya gama, sai mawaƙi Ɗan Baiwa daga Jihar Taraba ya nishaɗantar da taron da waƙa ta musamman da ya rera wa ƙungiyar.
Sai kuma Missis Laureta Markus, darakta a Hukumar Al’adu ta Jihar Kaduna, da Missis Blessing daga Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kaduna suka yi jawaban fatan alheri ga ƙungiyar, kuma suka bada shawarwari ga ‘yan ƙungiyar da Kannywood baki ɗaya.
A daidai wannan gaɓar, aka tafi hutu, inda aka ci, aka sha, aka gyatse. An sada zumunci a lokacin, waɗanda suka jima ba su haɗu ba suka ga juna, suka yi farin ciki.
Bayan an dawo, sai baƙo na musamman, wato Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Maiyaƙi, ya gabatar da jawabin ƙaddamarwa inda ya ce: “A duniya baki ɗaya, ƙasar Indiya ita ta fi kowa yawan yin finafinai a duniya, bayan ƙasar Indiya sai Nijeriya da ke Nollywood. Nijeriya ta fi Hollywood yawan finafinai da ake yi a duniya.
“A Nollywood, Kannywood a bisa ƙididdiga ya nuna cewa ana finafinai 2,500 a Nijeriya. Cikin 2,500 ɗin nan ƙididdiga ya nuna cewa finafinai da suka shiga rekod, wanda suke zuwa Hukumar Tace Finafinai aka yi masu rajista, ba wanda ake yi a ko’ina ba, guda 1,000 daga Kannywood suke zuwa. In ka ce cikin dubu biyu, ana yin dubu ɗaya daga Kannywood, kenan rabin fim a Nijeriya daga Kannywood suke zuwa.

“Amma abin takaici, finafinan da ake yi a Kannywood, a yankin Arewa, ba su da tasirin da ake samun kuɗaɗen shiga, saboda kuɗaɗen shigan su na taimakawa wajen ɗaga GDP, wanda GDP ɗin nan yana nufin wani wuri ne da gwamnati ke samun kuɗaɗen shiga.
“In za mu faɗa kan mu gaskiya, za ka ga mutum a fim, amma in ka gan shi a zahiri sai ka tausaya masa saboda fim ɗin da ake yi ba ya tsananta masa komai.
“A shekarun baya an samu wadda a duk fitowa ɗaya ana ba ta dubu uku, in ta gama yin fim ɗin baki ɗaya wataƙila ta samu dubu talatin da wani abu. A yanzu abin da na ke yi, ina zaburar da mu ne mu yi abin ɗaya dace, mu ɗauki sana’ar da daraja.
“Sannan a Kannywood ba mu da haɗin kai, ba mu so mu taimaki kan mu. Dole ne mu faɗa wa kan mu gaskiya.
“A matsayin mu na gwamnati, in Allah ya yarda za mu yi taro, ma’aikatar za ta ba da gudunmawa, dole a riƙa yin master classes domin fim ɗin mu ya dace da sauran finafinan duniya. Shi ne zai taimaka a samu abin da ake so.
“Ga shi na ga Kanawa daban-daban, ga wani daga Taraba, sannan mu ‘yan Kaduna ba mu ɗauki wannan abu da muhimmanci ba.
“Saboda haka ina kira gare ku, ina kuma tabbatar maku, a ƙarƙashin mai girma Gwamna Uba za ta bada gudunmawa don tabbatar da cewa an farfaɗo da wannan harka. Gwamnati za ta amfana, ku za ku amfana.
“Saboda haka ya zama wajibi mu ɗauki wannan abu da muhimmanci. Ina fatan a shekara mai zuwa kamar wannan lokacin, za mu zo muna farin ciki domin wannan ɗakin taron zai yi mana kaɗan.
“Kuma ina tabbatar maku cewa wannan Ma’aikata ta Yaɗa Labarai za mu taka rawar da ya kamata mu taka, a gayyato manyan mutane, za kuma a yi shi cikin tsari. Daga nan zuwa wannan lokaci ƙungiya ta ƙara ƙarfafa. Na gode, Allah ya sa mu tashi lafiya.”

Da ya gama, sai aka ƙaddamar da ƙungiyar tare da rantsar da shugabannin Kwamitin Amintattu da shugabannin ƙungiyar, wanda shi kwamishina ya rantsar da su.
A ƙarshe, Darakta-Janar na ƙungiyar, Alhaji Adamu Bello (Ability) ya yi jawabin godiya ga manyan baƙi da sauran mahalarta taron.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 12:15 na dare.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Sani Sule Katsina, Isah A. Isah, Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj, Kwamared Rabe Lemoo, Ɗandoso Godowoli, Malam Al-Amin Ciroma, Ibrahim Daddy, Malam Sabi’u Gidaje, Auwal Ɗanja, Abubakar Hunter, Hajiya A’isha B. Umar, Hajiya Fatima Kadashi, darakta Mannir K-Eza, Malam Aminu Dagash, da sauran su.
![]()







