• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba

by ABBA MUHAMMAD
October 25, 2025
in Labarai
0
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba

Alhaji Adamu Bello (Ability), Shugaban KAFIGAN

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DARAKTA-JANAR na sabuwar ƙungiyar nan ta masu shirya finafinai ta Nijeriya mai suna KAFIGAN, Alhaji Adamu Bello (Ability), ya miƙa saƙon godiyar sa ga mahalarta taron ƙaddamar da ƙungiyar da rantsar da shugabannin ta wanda aka yi a jiya Juma’a.

An yi babban taron a ɗakin taro na otal ɗin Epitome da ke unguwar Barnawa, Kaduna.

A jawabin godiyar tasa, Ability ya ce, “Haƙiƙa yau rana ce ta farin ciki a gare mu, rana ce ta farin ciki ga duk wani wanda yake son ganin an inganta al’adun mu a Arewa da kuma Nijeriya.

“Abin alfahari ne ga duk wani wanda yake son ya ga an samar wa mutane ayyukan yi ta hanyoyin da suka dace.

“Duk da yake an ce ni ina yi jawabin godiya ne, kuma zan yi iya ƙoƙari in tsaya a nan in miƙa godiyar. Amma kafin in fara gode wa kowa, ina ganin ya kamata Ku taya ni yi wa Allah (s.w.t.) godiya da Allah ya sa dukkan mu nan muka baro gidajen mu, muka zo Kaduna lafiya. Muna roƙon Allah (s.w.t.) yadda ya kawo mu nan lafiya, Allah don girman sa, don zatin sa, ya maida kowa gidan sa lafiya.”

Ya ci gaba da cewa, “Godiya ta biyu, zan yi godiya ga gwamnatin Jihar Kaduna domin ba don dangantakar mu da mai girma Kwamishina ya sa ya zo nan ba, Allah ya kai shi ma’aikatan da ya dace, domin shi ƙwararren ɗan jarida ne, ya yi aiki a ma’aikatu na watsa labarai na ƙasashen duniya da dama, kafin ya dawo Nijeriya, ya zo yanzu yake bada gudunmawar sa, ku sani, wannan bawan Allah yana da lokaci ne ƙanƙani. Menene lokaci ƙanƙani? Yau ne muke tare da shi, babu mamaki Allah ya ce gobe akwai inda ya fi muhimmanci a gare shi, ko kuma mai girma gwamna ya ce akwai inda ya fi nan bari ya maida shi. Don haka mu yi ƙoƙari mu amfana da ɗan wannan lokaci da Allah ya ara masa mu taimaki wannan masana’antar.

“Yayi mana gugar zana a kan abubuwa guda uku, wasu ba su fahimta ba, wasu sun fahimta, amma ba su ɗauki abin kamar wasa ne. Abin baƙin ciki ne ga mutumin da Allah ya yi wa baiwa, ya yi wa basira, ya yi wa hikima, kuma yana amfani da wannan damar wurin taimaka wa al’umma, wajen faɗakar da su, wayar da su da kuma faɗakar da su, amma abin baƙin ciki a ce yau rashin lafiya ya kama shi, sai an riƙa zuwa gidajen rediyo ana talla, ana neman taimako a tallafa masa.

“Wannan abin baƙin ciki ne, abin takaici. Sana’ar mu sana’a ce da ya kamata a ce muna taimaka wa wasu a duniya, ba wai ake taimaka mana ba. To wannan yana nuna cewa ne sai mun maida hankali, mun dubi sana’ar ta hanyar da ta dace domin mu inganta ta.

“Na biyu, akwai ɓangaren addini da za ka ga ana yi wa masu wannan harkar mummunar fahimta. Wannan tsari ne da ya kamata a fito a faɗa wa juna gaskiya, ina ne ya kamata a yi gyara, ina ya kamata a yi kaza, me zan yi in gyara addini na, me zan yi in gyara al’ada na ko in taimaki al’ada na, me zan yi in gyara tarbiyya na ‘ya’ya na da sauran al’umma? Wannan shi ne tsarin, wannan shi ne tunanin.

“Wasu suna ganin kamar an kafa ƙungiya ne kawai don sharholiya. Wannan ƙungiya ba mu kafa ta don sharholiya ba, shi ya sa muka ɗebi masana, waɗanda suka san abin da suke yi. A wannan ƙungiyar muna da farfesoshi uku, daktoci shida. Alhaji ba za ka yi karatu tun daga sakandare har ka kai PhD a ce kai wawa ne ba ka san abin da kake yi ba, ba zai yiwu ba.

“Akwai iyaye wanda sun san tarbiyya, sun san me suke yi. Wannan zaɓi ne muka yi domin mu taimaki wannan sana’ar. Kuma ina Allah ya yarda zai taimake mu.”

Ya ce, “Saboda haka ‘yan’uwa zan ci gaba da godiya. Yadda na gode wa mai girma gwamna, zan gode wa mutum biyu wanda ba don su ba wannan taron da bai yiwu ba.

“Na farko akwai Ministan Tsaro, Alhaji Badaru Abubakar, wanda da taimakon Allah da gudunmawar sa, wannan taron ya tabbata.

“Na biyu, akwai wata baiwar Allah daga Jihar Gombe, Hajiya Fatima Bintu Bello, wanda tsohuwar ‘yar Majalisa ce ta Tarayya, a halin yanzu Shugabar Ƙaramar Hukuma ce a Gombe. Baiwar Allahn nan ta taimake mu da taimakon Allah da taimakon ta, wannan taron ya tabbata.

“Sannan na uku, akwai Kwamishina daga Jihar Katsina, Alhaji Hamza Sule Faskari, da taimakon Allah da taimakon sa, wannan taro da muke yi a nan ya tabbata.

“Don haka wajibi ne, duk wanda ya yi maka abin da ya dace, ka yi masa godiya, kuma ka jinjina masa, ba don komai ba sai duk abin da mutum ya yi maka na alheri ka nuna ka ji daɗi.

“A ƙarshe, zan yi amfani da wannan dama in miƙa godiya ga dukkan waɗanda suka taimaka taron nan ya tabbata. Allah ya saka masu da alkhairi. Allah ya ba mu nasara, Allah ya maida kowa gidan sa lafiya.

Loading

Tags: Adamu Bello AbilitygodiyajawabiKadunaKAFIGAN
Previous Post

Za mu yi aiki da KAFIGAN, inji gwamnatin Kaduna a wurin ƙaddamar da ƙungiyar 

Next Post

Marubuta sun yi taron addu’a ga Hauwa Lawan Maiturare a Kano

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Marubuta sun yi taron addu’a ga Hauwa Lawan Maiturare a Kano

Marubuta sun yi taron addu'a ga Hauwa Lawan Maiturare a Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!