CIKIN alhini da jimami, gamayyar ƙungiyoyin marubuta na Jihar Kano sun gudanar da taron Dandalin Marubuta na musamman domin tunawa da marubuciya Hauwa Lawan Maiturare wadda Allah ya yi wa rasuwa a farkon watan Satumba da muke ciki.
Ƙungiyoyin sun haɗa da ANA, HAF, da kuma GAMJIK sun haɗu ne a ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Kano.
Taron Dandalin Marubutan wanda reshen ANA ɗin ya saba gudanarwa a duk Asabar ɗin ƙarshen kowane wata, a yau ya kasance na zaman juyayi da addu’a ne ga marigayiya Hauwa.
Taron, wanda aka aka gudanar a ɗakin karatu na Jami’ar Khalifa Isyaka Rabi’u (KHAIRUN), ya samu halartar marubuta da dama.
Tun da farko da yake bayanin manufar taron, Shugaban taron, Malam Zahraddin Ibrahim Kalla, ya bayyana ce: “Duk da yake mun saba zama a duk Asabar ɗin ƙarshen wata domin gudanar da Dandalin ANA na Turanci, to a wannan zama mun karkata taron ne domin jimami da alhini na rashin ɗaya daga cikin mu, wato Hauwa Lawan Maiturare, wadda Allah ya yi wa rasuwa.
“Don haka wannan zama na Haɗakar ƙungiyoyin marubuta ne na Jihar Kano, kuma a wannan zama duk labari ko waƙoƙin da za mu gabatar ya shafi rasuwar Hauwa Lawan Maiturare, saboda mun ware zaman taron ne domin ta, mu tuna da ita, mu yi alhinin rasuwa tare da yi mata addu’a.”
Bayan buɗe taron dai an fara karatun labarai ne, inda Ayuba Muhammad Ɗanzaki ya gabatar da labarin sa mai suna ‘Soyayya Da Kaddara’, wanda ya sadaukar ga Hauwa. Labarin na alhini ne da kuma taɓa zuciya.
Bayan shi, sai M.U .Ganduya gabatar da waƙa da Turanci mai suna ‘Life is Hard’.
Malam Nasiru Usman Babaye shi ma ya gabatar da waƙar sa mai suna ‘Ta’aziyyar Maiturare’. Waƙar tana da baitika 11 ɗauke da ɗimbin hikima da basira. A baitun farko ya bude da cewa:
“Roƙon ka muke yi ya Ilahi,
Don baban su Batulu Mahi,
Ayyukan ta su zamma cikin salahi.”
Waƙar ta tafi ne da jimami da kuma addu’a ta neman gafara a gare ta.

Shi ma Malam Khalid Imam ya gabatar da waƙar sa mai taken ‘Zane Na’, inda ya maƙala hoton sa a jikin waƙar mai salo irin waƙar Aƙilu Aliyu.
Dakta Murtala Uba Mohammed kuma ya karanta waƙa mai suna ‘Mutuwa’ wadda ya buɗe da cewa:
“Wadda ba ta barin mutane,
Ta bi kowa ta buge shi.
Wadda ba sauri take ba.
Mai tsawon rai tai jiran shi.”
Malam Nasiru G. Ahmad ‘Yan’awaki ya gabatar da waƙa mai taken ‘Ta’aziyyar ‘Yar’uwa Marubuciya’.
Zubairu Balannaji da ya gabatar da labari mai taken ‘Agola’.
Haka dai dandalin ya kasance na tsawon wuni guda ana gabatar da waƙoƙi da labarin ƙirƙira duk don tunawa da gudunmawar da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare.
A ƙarshe an rufe taron da addu’a ga marigayiyar da sauran dukkan Musulmi baki ɗaya.
![]()







