A RANAR Alhamis, 11 ga Disamba, 2025 aka gudanar da taron karrama matan da suka yi nasara a gasar rubutun gajerun labarai ta mata ta Hikayata ta bana, gasar da BBC Hausa ke gabatarwa a duk shekara. Wannan ita ce shekara ta 10 da aka yi gasar. Fadila Lamiɗo ce ta zamo gwarzuwar gasar ta 2025. Waɗanda suka rufa mata baya a matsayin ta biyu da ta uku su ne Jamila Lawal Zango da Hafsat Sani Tanko.
Fadila, wadda ‘yar Kaduna ce, ta samu kyautar naira miliyan ɗaya da satifiket ɗin shaidar nasarar da ta samu daga BBC Hausa.
Mujallar Fim ta tattauna da Malama Fadila Lamiɗo domin jin tarihin ta, yadda ta fara rubutu, da kuma yadda ta samu kan ta a matsayin wadda ta zo ta ɗaya a gasar Hikayata ta wannan shekarar.
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
FADILA LAMIƊO: To, farko dai suna na Fadila Lamiɗo, kuma ni haifaffiyar Jihar Kaduna ce. Na yi karatu zuwa matakin difloma.
FIM: Ya aka yi kika shiga harkar rubutu?
FADILA LAMIƊO: Na kasance mai yawan karatun littattafan Hausa, don haka lokacin da na ga an fara rubutun onlayin na yi tunanin jarabawa, don da ma akwai labarin da yake cikin kai na tuni wanda na sha ɗaukar biro da takarda in fara rubuta shi a littafi amma ba na wuce shafi biyu zan a jiye shi. Amma a shekarar 2016 na saki shafi ɗaya a onlayin, cikin ikon Allah sai na ga jama’a na ta jiran cigaban sa. Wannan ya ba ni ƙwarin gwiwar rubuta shafi na gaba; daga haka kuma shi kenan har hannu ya nuna.


FIM: Ko a lokacin da kika fara rubutu kin samu wani ƙalubale?
FADILA LAMIƊO: Gaskiya ni dai a lokacin da na fara rubutu babu wani ƙalubale da zan ce na fuskanta, don ina faɗa ina ƙara faɗa ban fara rubutun da niyyar in zama marubuciya ba, kawai na ga ana rubutu onlayin ne na ce bari in jaraba rubuta labarin da ya daɗe a cikin kai na in ji me za a ce a kai. Da a ce na hango wani ƙalubale wataƙila da ban ci gaba da rubutun ba, gaskiya, don ni a lokacin ban san ma ina da baiwar rubutun ba, na ɗauka kawai na yi jagwalgwalo na ne, amma sai na ga makaranta har da marubutan ma suna ta magana a kan labarin.
FIM: Ko kin taɓa buga littafi wanda ya shiga hannun mutane?
FADILA LAMIƊO: Na taɓa buga littafi na guda ɗaya mai suna ‘Muguwar Miya’.
FIM: Ko kina cikin wata ƙungiyar marubuta?
FADILA LAMIƊO: E, ina yi. Ina cikin ƙungiyar Adabi Writers Association.

FIM: Wannan shi ne karo na farko da kika fara shiga gasar Hikayata ko a baya kin taɓa shiga?
FADILA LAMIƊO: E, na taɓa shiga gasar a shekarar 2022 (amma) ko a matakin farko labarin bai fito ba. Ban sake shiga ba sai a 2024; a wannan karon ma bai shiga ko matakin farkon ba. Sai a shiga ta uku a wannan shekarar Allah ya ba ni nasara.
FIM: Da man kin sa rai a kan za ki ci gasar?
FADILA LAMIƊO: Ko kaɗan wallahi ban sa rai ba. Ana saura kwana shida a rufe gasar wata marubuciya ta matsa mani sai na shiga, na ce mata lokaci ya ƙure. Ta ce, “Idan kin sa niyya bai ƙure ba.” Cikin ikon Allah sai ban yi musu ba, na ce to. Sai bayan na tura ma na ce mata na tura. Tun da na tura kuma ban sake ma ko tuna labarin ba, harkoki na kawai na ci gaba da yi, sai da aka sanar mani labarin ya yi nasara sannan na binciko shi na sake karantawa.
FIM: Da kika samu labarin rubutun ya fito a matakin ƙarshe, ya kika ji a lokacin?
FADILA LAMIƊO: Anya farin cikin da na ji zai misaltu kuwa? Da yake an sanar ni da daddare ne, don haka daren nan ban iya runtsawa ba, yadda na ga rana haka na ga dare. Ban tabbatar da farin ciki yana hana barci ba sai a ranar. Haka na kwana ina gode wa Allah, don gasar Hikayata babbar gasa ce wadda dubannan jama’a suke shiga, a ce naka labarin ya shiga matakin ƙarshe wannan babban al’amari ne.

FIM: A lokacin da aka tabbatar da ke ce kika zo ta ɗaya a gasar, ya kika ji?
FADILA LAMIƊO: Na ruɗe sosai har ina jin kamar ƙafafuwa na ba za su iya ɗauka ta ba, don ni ban taba bai wa kai na zan zo ta ɗayar ba, duk da cewa tun kafin a sanar marubutan da nake tare da su sun hasaso hakan, sai dai ni ban sa wa raina ba, domin ni ko ta ukun na zo babbar nasara ce a waje na. Waɗanda suke yin nasara a ƙananan gasanni ma suke murna suna alfahari bare wadda ta zo ta uku a gasar Hikayata, nasara ce babba, sai kuma gashi na samu nasarar zamowa ta ɗaya. Godiya ta tabbata ga Ubangiji na mai iya yin komai a lokacin da ya so ba tare da ya yi shawara da kowa ba.
FIM: A yanzu da kika lashe wannan gasar burin ki ya gama cika a harkar rubutu ko akwai wani burin da kika saka a gaba?
FADILA LAMIƊO: A cikin kowane irin yanayi Ina cewa ne alhamdu lilah. Amma ina sha’awar in ga na ƙware sosai a rubutun fim. Wannan kusan zan iya cewa shi ne buri na a yanzu.
FIM: Waɗanne irin matakai ya kamata marubuta su bi domin yin nasara a harkar rubutu?
FADILA LAMIƊO: Mata marubuta su jajirce su yi aiki tuƙuru su kuma rinƙa yin bincike, wannan zai taimaka ƙwarai da gaske.

FIM: A yanzu marubuta mata sun fi maza yawa. Ko ya kike kallon hakan a mataki na cigaba?
FADILA LAMIƊO: To ai daidai kenan, mai ido ɗaya ya leka buta, ba ana cewa mata sun fi maza yawa a duniya ba? Haka ya dace a ko’ina ma sai a ga mata sun fi yawan. Wannan cigaba ne.
FIM: To madalla, mun gode.
FADILA LAMIƊO: Ni ma na gode.
![]()







