• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Baɗala: Hukumar Tace Finafinai ta dakatar da jaruma Samha Inuwa kan zargin shigar banza da wallafa batsa

by ALI KANO
January 5, 2025
in Labarai
0
Baɗala: Hukumar Tace Finafinai ta dakatar da jaruma Samha Inuwa kan zargin shigar banza da wallafa batsa

Samha M. Inuwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da fitacciyar jarumar Kannywood kuma furodusa, Samha M. Inuwa, bisa zargin rashin ɗa’a wajen saka sutura da kuma wallafa abubuwan batsa a soshiyal midiya, tare da wasu laifuffuka makamantan haka.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa an dakatar da jarumar ne bayan ta yi kunnen uwar shegu da gargaɗi da dama da aka yi mata, a rubuce da na baki.

Ya ƙara da cewa baya ga dakatarwar wadda za ta ɗauki tsawon shekara guda, hukumar ta kuma soke lasisin aikin ta, tare da sanar da cewa za ta hukunta duk wani furodusa da ya fito da ita a kowane fim a tsawon wa’adin dakatarwar.

Ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan an sha gargaɗin Samha kan yadda take yin shiga marar ƙima da kuma nuna halaye marasa dacewa, amma ta ci gaba da karya ƙa’idojin hukumar, wanda hakan ya sa aka yanke shawarar dakatar da ita.

Abdullahi ya bayyana cewa dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take, ta biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da dama da hukumar ta karɓa daga jama’a da masu kishin Jihar Kano dangane da halayen jarumar da suka saɓa wa dokoki da ƙa’idojin hukumar.

Ya ce: “Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano tana da hurumin doka na tabbatar da cewa duk bidiyo, rubuce-rubuce da sauran hanyoyin bayyana ra’ayi sun yi daidai da addini, al’adu, ƙa’idoji da darajojin jihar.

“Haka kuma hukumar ta soke izinin hulɗar ta tare da dakatar da tace duk wani fim da ta fito a ciki.

“Wannan dakatarwar wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar na ci gaba da tsare kyawawan ɗabi’u a masana’antar Kannywood da kuma tabbatar da bin duk ƙa’idoji da dokokin hukumar.

“Baya ga dakatarwar, hukumar ta soke lasisin aikin ta tare da dakatar da tace duk wani fim da jarumar ta fito a ciki.

“Wannan dakatarwar na daga cikin manufofin sabon shugabancin hukumar ƙarƙashin Abba Al-Mustapha na dawo da martaba da daidaito a masana’antar shirya finafinan Hausa.”

Loading

Tags: AbdullahiSaniSulaimanbaɗaladakatarwaHukumarTaceFinafinaiKanoSamhaMInuwaShigarBanza
Previous Post

Zaɓen MOPPAN: Ciyamomi da ‘yan takara sun yi taron fahimtar juna

Next Post

Zaɓen MOPPAN: Kwamiti ya fitar da tsarin yadda za a yi babban taro da zaɓe a Nassarawa 

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Zaɓen MOPPAN: Kwamiti ya fitar da tsarin yadda za a yi babban taro da zaɓe a Nassarawa 

Zaɓen MOPPAN: Kwamiti ya fitar da tsarin yadda za a yi babban taro da zaɓe a Nassarawa 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!