ƘUNGIYAR masu harkar finafiinai ta Najeriya, wato Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), ta bayyana jin daɗin ta kan shirin da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano tare da Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) suka ƙaddamar domin yi wa ’yan Kannywood rajistar inshorar lafiya.
A cikin wata sanarwa da shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Shehu Hassan Kano, ya sanya wa hannu a ranar 5 ga Yuni, 2026, ƙungiyar ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan wani muhimmin zama da aka gudanar a ranar Alhamis, 4 ga Yuni, tsakanin Hukumar Tace Finafiinai ta Jihar Kano da KSCHMA.
MOPPAN ta ce babban sakataren Hukumar Tace Finafiinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, shi ne ya jagoranci tawagar masana’antar zuwa wajen Babbar Sakatariyar KSCHMA, Hajiya Rahina, inda aka tattauna hanyoyin tallafa wa ’yan Kannywood, musamman waɗanda ke fama da matsalolin lafiya.
MOPPAN ta ce daga cikin matakan farko da aka ɗauka akwai fara kula da wasu fitattun jarumai da ke fama da matsalolin lafiya, ciki har da Aminu Mahiru, Haruna Titibiri, Ladidi Fagge, Abubakar Hunter, Mustapha Musty, Zainab Golden da kuma Zakiyya Ibrahim.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa an riga an fara rabon fom ɗin rajistar inshorar lafiyar, tare da kammala wasu daga cikin matakan da suka dace domin fara aiwatar da shirin.
An bayyana cewa duk wani ɗan Kannywood da ya cika fom ɗin zai samu damar cin gajiyar kulawar lafiya a asibitocin da aka amince da su ƙarƙashin tsarin.

A cewar ƙungiyar, za a gudanar da bikin ƙaddamar da shirin mai suna “Kannywood Abba Health Care” a nan gaba kaɗan, inda ake sa ran manyan jami’ai da wakilan ƙungiyoyin Kannywood da suka haɗa da MOPPAN, Arewa Elders, Actors da KAFIGAN za su halarta.
Shugaban MOPPAN na ya yaba wa El-Mustapha bisa ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa masana’antar Kannywood, yana mai cewa wannan shiri wata babbar gudunmawa ce da za ta taimaka wajen inganta walwala da jin daɗin masu sana’ar finafinai.
Ya kuma yi kira ga dukkan ’yan Kannywood da su rungumi wannan dama ta rajistar inshorar lafiya domin tabbatar da samun kariya da kulawar lafiya a duk lokacin da buƙata ta taso.
![]()







