FITACCEN jarumin Kannywood kuma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Harkokin Matasa, Alhaji Sani Musa Danja, ya kammala ginin sabon gidan sa na zamani da ke birnin Kano.
Kimanin shekaru huɗu da suka gabata ne Sani Danja ya rushe tsohon gidan sa da nufin sake ginawa cikin sabon salo da ya dace da zamani. Sai dai tsawon lokacin da aikin ya ɗauka ya jawo ce-ce-ku-ce da ra’ayoyi mabambanta daga wasu mutane, inda wasu suka riƙa hasashen dalilan jinkirin kammala aikin.
Sai dai karin maganar Hausawa da ke cewa “Sannu ba ta hana zuwa” ta tabbata a wannan karo, domin a yanzu jarumin ya kai ga kammala ginin cikin ƙayatarwa da inganci.
Sabon gidan na Sani Danja yana unguwar Badawa Layout, a Ƙaramar Hukumar Nasarawa, cikin birnin Kano. Gini ne mai hawa biyu wanda aka tsara shi da salo na zamani, tare da kayayyakin more rayuwa masu inganci.

An ware sashe na musamman domin saukar baƙi, akwai wurin shaƙatawa, tare da ɗakunan wanka na zamani da sauran abubuwan da ke ƙara wa gidan armashi da annashuwa.
Da wannan sabon gida, ana iya cewa Sani Danja ya shiga sahun fitattun jarumai da mawaƙan Arewa masu gidaje na alfarma a Kano, ciki har da Aminu Saira, Ali Jita, Dauda Kahutu Rarara da Naziru Sarkin Waƙa.




![]()







