KAMFANIN gidan talbijin na Tozali ya bayyana cewa zai gudanar da bikin Henna Ball & Tozali People’s Awards 2026 domin karrama masu ƙwazo, jajircewa da gudunmawar jinƙai, tare da tallafa wa mata da suka tsira daga hare-haren ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
An tsara bikin, wanda taken sa shi ne “Ƙarfafa gwiwar waɗanda suka tsira. Maido da bege,” a ranar 31 ga Oktoba, 2026, a wurin taro na Los Angeles Event Centre da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Abuja yau Asabar, bikin zai haɗa jami’an gwamnati, ’yan kasuwa, masu ƙirƙire-ƙirƙire, ’yan fim da nishaɗi, masu taimakon jama’a, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki, domin karrama mutane da ƙungiyoyin da ke bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma.
Masu shirya bikin sun ce za a karrama waɗanda suka yi fice a fannoni da suka haɗa da aiki tuƙuru da sadaukarwa, juriya da dagewa, ƙirƙire-ƙirƙire, baiwa da ƙwazo, tare da ba da kulawa ta musamman ga wasu jaruman da ba a cika gane irin gudunmawar da suke bayarwa ba wajen kawo sauyi a cikin al’ummomin su.
Baya ga bayar da lambobin yabo da nishaɗi, kamfanin Tozali TV ya ce bikin zai mayar da hankali kan ayyukan jinƙai, inda za a ƙara wayar da kan jama’a da kuma tara tallafi domin farfaɗo da rayuwa da ƙarfafa mata da suka tsira daga garkuwa da mutane, hare-haren ’yan bindiga da Boko Haram.
Za a gudanar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar gidauniyar Tozali Girl Child and Women Foundation da sauran abokan hulɗar da abin ya shafa.
Da take magana kan manufar bikin, Shugabar kamfanin Tozali TV, Hajiya Maimuna Yaya Abubakar, ta ce an tsara Henna Ball ne domin ya wuce batun biki da karramawa kawai.
Ta ce: “Henna Ball da Tozali People’s Awards ya wuce bikin murna kawai; dandali ne na karrama jarumtaka, faɗaɗa labarai masu kyau, da tunatar da waɗanda suka tsira cewa rayuwar su da burin su suna da muhimmanci.”
Ta ƙara da cewa taron zai haɗo al’umma, shugabanni da ƙungiyoyi domin ƙarfafa waɗanda suka tsira da kuma maido musu da bege.
Bikin na bana zai kuma baje kolin al’adun Nijeriya, kayan sawa, nishaɗi da masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire, tare da samar da damar haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a gwamnati, kasuwanci, kafafen yaɗa labarai, fasaha da ayyukan jinƙai.
Kamfanin Tozali TV ya yi kira ga ƙungiyoyi, cibiyoyi, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane masu sha’awar ƙarfafa al’umma da inganta rayuwar jama’a da su haɗa gwiwa da wannan shiri.
Masu shirya bikin sun bayyana taron a matsayin wani dare na murna da ƙarfafa gwiwa, wanda zai haɗa karrama ƙwazo da ƙoƙarin tallafa wa waɗanda suka tsira kuma suke cikin mawuyacin hali, tare da taimaka musu wajen sake komawa cikin al’umma da samun ƙarfin dogaro da kan su.
![]()





