AN ɗaura auren fitaccen daraktan Kannywood, Malam Aminu Saira, da sahibar sa, Maryam Mahmoud Muhammad, a Azare, Jihar Bauchi.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2 na rana a yau Juma’a, 31 ga Yuli, 2026, a Babban Masallacin Juma’a na Azare.
Manyan jarumai, daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood tare da ’yan’uwa da abokan arziki sun je garin domin halarci bikin.

Tun a jiya Alhamis wasu daga cikin manyan baƙin suka isa garin, inda aka gudanar da liyafar cin abinci a dare a NINADS Events Centre. Sun haɗa da Abdul Amart, Kamal S. Alƙali, Garzali Miko da Ali Gumzak, tare da ɗimbin sauran baƙi maza da mata.

Mawaƙan Kannywood, ƙanen ango Naziru M. Ahmad da Nazifi Asnanic, sun nishaɗantar da mahalarta da waƙoƙin su a yayin liyafar.
Da wannan aure, Saira ya zama mai mata biyu kenan, domin yana da uwargida mai suna Aisha.
Bikin ya ja hankalin ’yan Kannywood da sauran jama’a su.

![]()







