• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kama Mu’azzam: Afakallah ya yi wa su Falalu Ɗorayi da Baban Chinedu raddi

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
February 20, 2021
in Labarai
0
Kama Mu’azzam: Afakallah ya yi wa su Falalu Ɗorayi da Baban Chinedu raddi
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya yi martani ga ‘yan Kannywood masu sukar sa kan kama furodusa kuma darakta a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Mu’azzam Idi Yari, ya ce mutane ne waɗanda ba su son bin doka da oda.


Mujallar Fim ta ruwaito cewa irin masu sukar tasa sun haɗa da fitattun jarumai Falalu Ɗorayi, Baban Chinedu, Ummah Shehu, furodusa Abdul Amart Maikwashewa, mawaƙi Nura M. Inuwa da wasu da dama.


Afakallah ya ce to su sani “ba gudu ba ja da baya” a kan kama duk wani wanda ya karya dokar hukumar, komai matsayin sa ko ɗaukakar sa a masana’antar Kannywood.


Ya yi nuni da cewa an kama Mu’azzam tare da gurfanar da shi a gaban kotu ne saboda ba ya da takardar izinin shirya fim a Jihar Kano kamar yadda doka ta tanada.


An dai kama Mu’azzam ne a shekaranjiya Alhamis, 18 ga Fabrairu, 2021 a lokacin da ya ke ɗaukar wani sabon fim a Kano.

Jami’an hukumar sun kai samame a lokeshin ɗin domin ganin idan ya na da takardar shaidar ɗaukar fim (film shooting permit) wadda hukumar ke ba waɗanda su ke son ɗaukar fim a jihar.


Bayan dirar jami’an a lokeshin ɗin, sai su ka gayyaci daraktan domin ya amsa tambayoyi a ofishin su. 


Da su ka tambaye shi ya nuna takardar shaida bai nuna ba, sai kawai su ka yi awon gaba da shi zuwa kotun musamman bisa tuhumar ya bijire wa dokar Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano. 


Tun daga lokacin kuwa ‘yan fim maza da mata su ke sukar Afakallah da hukumar sa, su na cewa kama Mu’azzam da aka duk siyasa ce. Sun tura saƙwannin adawa da kamun da aka yi masa a soshiyal midiya, har wasu na addu’ar ganin bayan Afakallah daga kan muƙamin sa.


Abdul Amart ya ce: “Wannan zalunci ne ƙarara, kuma wallahi bambancin siyasa ya sa akai mai haka.”

A wani saƙon da ya aika a shafin sa na Instagram kuma, Amart ya yi nadamar yadda yawancin manyan Kannywood su ka yi gum da bakin su kan wannan al’amari, ya ce tumasanci ne ya janyo haka da kuma ganin cewa Mu’azzam bai da kuɗi kuma “bai zamani”.


Shi kuma Falalu A. Ɗorayi ya yi dogon rubutu a Instagram inda ya ce, “Idan da gaske ne, Mu’azzam Idi Yari ya na da takardar damar yin aiki a Kano, Hukumar ta ba shi. Sannan aikin da aka kama shi a kai shi ma suna da takardar gabatarwa, furodusa ya karɓo daga hukumar.


“To meye dalilin kamawar da ɗaurewar?Zalinci, tozarci ko cin zarafi?


“A cikin ukun nan, babu wanda ya ke ɗorewa mai yin sa da alkairi.


“Amfanin biyayya shi ne ta zamar maka gata a gurin wanda ka ke wa, wala mutum Ko gwamnati.

“Kullum ina faɗi, maslaha ita ce hanyar gina kyakkyawar alaƙa.Zuciyar ‘sai na rama’ ba ta haifar da abu mai kyau, sai ƙarin abokan gaba.


“In mutum yai maka laifi ‘personal’, ku yi shari’a ‘personal’, kar kai amfani da ƙarfin kujera ko umarnin zuciya ko umarnin wasu. Hakan ke haifar da rashin adalci a hukunci.


“A ƙarshe, ina ba wa shugabannin Kannywood shawara su sake buɗa maganar shigar da ƙarar hukumar a ‘High Court’ domin a sami fashin baƙin matsayin hukumar da ‘ya’yan ta.


“Gudun kar a ringa yin kitso da kwarkawata. ‘Ya’yan ku na da ‘permit’, amma ana ɗaure su.


“Allah ya kyauta. Amin.”

Shi kuwa Akallah, a martanin da ya yi wa masu sukar tasa, ya bayyana wa mujallar Fim cewa, “Hukumar ta gayyace shi (Mu’azzam) domin ya zo ya gabatar da kan sa a kan abin da ake tuhumar sa da shi, inda ya zo bai bada takardar da hukumar ta tanada ba ga masu son ɗaukar fim a Jihar Kano. 


“To sai dai hukuma ba yadda za ta yi illa ta miƙa shi zuwa kotu. Haka kuma aka yi, mu ka miƙa shi zuwa kotu wanda da kotu ta tambaye, shi bai bada takardun ba. Kuma da ya na da su ai ba zai ƙi ya miƙa ba.”


A kan masu zargin sa, shugaban hukumar ya ce, “Mutane za su iya faɗar maganganu, musamman waɗanda ba su yarda su bi doka ba kuma sun ɗauka cewa in sun faɗi magana kowa ya ji ta mutane za su ɗauka an yi zalunci ne, to don haka a nan tunda har an tafi kotu kuma ya je an nemi ya gabatar da cewa ga shi abin da ake tuhumar sa bai ba wa kotu cikakkun abubuwan da ake tambayar sa ba.” 


Afakallah ya yi kira da babbar murya ga masu son karya doka a jihar da su sani cewa “duk wanda ya taka wannan dokar, ko waye shi, komai matsayin sa kuma komai ɗaukakar da ya ke gani Allah ya yi masa, in dai ba zai girmama mutanen Kano a kan tsarin bin  wannan dokar ba, duk da wasu su na ganin ba za su bi dokar ba, to su sani cewa mu ma mu na nan ba gudu ba ja da baya ga duk wanda ya ce ba zai bi doka ba a jihar.”


Da mujallar Fim ta tambaye shi ko cewa akwai saɓani a tsakanin sa da Mu’azzam kamar yadda irin su Falalu ke cewa, sai ya ce, “Babu wata rashin jituwa. Kawai dai ya karya doka ne.”

Mu'azzam Idi Yari (a sama), da Isma'il Na'abba (Afakallah)
Mu’azzam Idi Yari (a sama), sai Falalu Ɗorayi (a hagu) da Yusuf Baban Chinedu a wani fim
Previous Post

Littafin koyon salatin Annabi cikin sauƙi

Next Post

Ministar Jinƙai ta jajanta kan mutuwar sojojin sama 7

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ministar Jinƙai ta jajanta kan mutuwar sojojin sama 7

Ministar Jinƙai ta jajanta kan mutuwar sojojin sama 7

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!