FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta ɓara game da wani jarumi da ta ke ganin ya fi kowane ɗan wasa takalar ta a soshiyal midiya.
Cikin ɓacin rai, jarumar ta kira shi da munanan kalamai da su ka haɗa da “ɗan wiwi”, “wawa”, “almajiri mijin almajira”.
A wani saƙon bidiyo da ta tura a Instagram a yau, Zee-Zee ta ce ta lura da cewa ba abin da jarumin ya fi yi kamar faɗin baƙaƙen maganganu game da ita a duk lokacin da aka wallafa wani labari game da ita.
Mujallar Fim ta lura da cewa ba shakka akwai wani jarumi ɗan Kaduna wanda ya fi kowane ɗan fim zaƙewa game da ita, musamman a shafin Instagram na mujallar inda ya kan faɗi kalamai na tsokana da takala a kan jarumar daga lokacin da ta yi barazanar za ta kashe kan ta.

A bidiyon da ta tura mai tsawon sakan 58, Zee-Zee ta yi ramuwar gayya inda ta ce a lokacin da ta ke kan ganiyar ta a industiri, shi wannan jarumi bai wuce matsayin yaro ɗan aike mai sawo mata ruwan sha ba.
Haka kuma ta yi shaguɓe game da matar jarumin, wadda Buzuwa ce.
Ga kalaman da Zee-Zee ta furta a matsayin raddi ga jarumin, kamar yadda mujallar Fim ta kwafo daga guntun bidiyon:
Ta ce: “Wannan bidiyo na yi ne domin in jawo wa wani ɗan wiwi ɗin akto da ke Kannywood fim industiri kunne domin ya fita a harka ta, domin na ga shi bai da aiki sai duk inda ya ga an sa hoto na a soshiyal midiya sai ya dinga shiga idan ya sha wiwin sa ya bugu ya dinga shiga ‘comments section’ ya dinga faɗar maganganun ɓatanci a kai na, da hali na da ba hali na ba, saboda kawai ya na so in tanka shi domin ya yi suna.
“To na gano ka! Ni Ummi Zee-Zee na fi ƙarfin ka. Sunan da na yi a fim industiri ba ka isa ka yi ba har ka mutu. Kuɗin da na yi a industiri ba ka isa ka yi shi ba har ka mutu! Ka gane?
“Wai ka manta lokacin da ina fim ka na fim kai ɗan siyo min fiyawata ne? Ƙazami ma irin ka, don yanzu ka samu ka goge?
“Matar aure ma sai sadaka-yallah aka samu aka jona ma!
“Wawa kawai, almajiri mijin almajira! Mtschww!”
Mutane da dama da su ka kalli bidiyon a shafin mujallar Fim sun ambaci sunan wani jarumi wanda su ka ce da shi Zee-Zee ta ke.
Duk da yake jarumar ba ta ambaci sunan sa ba, Hausawa sun ce duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda ya ke, sannan shi ma wanda aka zaga ɗin ya san da shi ake.
Mutane sun zuba ido su ga inda wannan badaƙalar za ta nufa.
![]()







