MATA ‘yan fim su na nan su na shirin yin wata gagarumar walimar cin abinci da Ƙaramar Sallah don su sada zumunci a tsakanin su.
An shaida wa mujallar Fim cewa ba a taɓa yin irin wannan walimar a masana’antar ta Kannwood ba.
Za a gudanar da walimar ne a ƙarƙashin Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeriya, wato ‘Kannywood Women Association of Nigeria’ (K-WAN).
Waɗannan bayanan sun fito ne daga bakin shugabar ƙungiyar K-WAN, Hajiya Hauwa A. Bello (Hauwa Edita), yayin da ta ke tattaunawa da mujallar Fim.
A tattaunawar, Hauwa Edita ta fara da miƙa godiya da sambarka ga mutanen da su ka taimaka wa ƙungiyar a cikin wannan wata na Ramadan.
Ta ce, ‘’Duk da gudunmawar da wasu daga cikin al’umma su ka ba wa wannan ƙungiya a wannan wata na Ramadan wanda su ka haɗa da Isma’il Na’abba (Afakallah), shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, wanda ya bada buhun shinkafa wanda aƙalla mutane goma sun amfana da ita; da Abdul Amart, shi ma ya bada shinkafar da mutum goma za su amfana wanda daga baya ya ƙara ba mu wani tallafin domin a taimaka wa waɗanda su ke da buƙata; ita ma ɗaya daga cikin matan wannan ƙungiya, Maijidda Bello Ado Bayero (‘Ɗan Mazari’), ta bada gudunmawar kuɗi N50,000, wanda kuma mu ka ba wa mata N2,500 su ashirin, duk da haka a cikin wannan ƙungiya mu na da mabuƙata da ya kamata a tallafa wa da yawa.

“To, sai dai duk da cewar wasu daga cikin shuwagabannin ƙungiyar su na jagorantar wasu ƙungiyoyin bada tallafin amma hakan bai sa sun taimaka wa wannan ƙungiya da azumi ba duk da cewar su na samu sosai, amma wasu waɗanda ba ‘ya’yan cikin ta ba ma su na yunƙurin bayarwa domin a taimaka wa masu buƙata da ke cikin mu.”
Da ta ke bayani a kan ɗaya daga cikin maƙasudin kafa ƙungiyar ta K-WAN, Hauwa ta ce, “Manufar wannan ƙungiya shi ne taimaka wa ‘yan ƙungiya har ta kai cewa yau waɗannan su ƙaru gobe waɗannan su ƙaru. To a bisa haka mu ka ƙudiri niyyar shirya wani gagarumin taro ko in ce walimar Sallah na farko tun bayan kafa ƙungiyar, wanda za a gudanar da wannan walima ƙarƙashin jagorancin Sakatariyar Tsare-tsare ta wannan ƙungiya, Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a), wanda mu ke so mu yi bikin Sallah, namu na mata zalla, domin mu jagoranci wani abu da ba a taɓa yi ba a masana’antar Kannywood, ta hanyar kiran mata – da masu aure da marasa aure, da waɗanda ake yi da su da waɗanda su ka shuɗe – domin ƙungiyar nan ta wakilci ko wace mata da ta taɓa yin wani abu a masana’antar. Kuma hakan na zuwa ne sakamakon irin daɗewar da aka yi ba a haɗu ba a gaisa da juna a yi zumunci, shi ya sa mu ka ga dacewar haɗa wannan walima.”
Shugabar ta ƙara da cewa ƙungiyar ba wai iya ta sanannun mata ba ce, a’a ta shafi kowa da kowa in dai mace ce kuma ta na cikin wannan masana’anta.
Za a gudanar da walimar dai a ranar Lahadi, 16 ga Mayu, 2021 da ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na dare a ɗakin taro na otal ɗin Ni’ima da ke Kano.
K-WAN ƙungiya ce da ta samu rijista a cikin 2019 kuma ta haɗa kafatanin matan da ke Kannywood, ciki har da masu ɗaukar nauyin shirya finafinai kimanin mata 20.