KYAKKYAWAR jarumar Kannywood, Fatima Ali Nuhu ta kan sanya zoben hanci jefi-jefi a yayin kwalliyar ta, kuma ta ce ta na “ɗan mararin son” hakan.
Jarumar, wadda ita ce babbar ɗiyar shahararren ɗan wasa Ali Nuhu, ta wallafa waɗannan hotunan a Instagram, inda ta samu yabon mabiyan ta.
Da alama, shi ma Ali ya yi na’am da hotunan domin kuwa ya sake wallafa ɗaya daga cikin su a nasa shafin na Instagram.

Fitattun jarumai mata irin su Fati Washa, Hafsat Idris, Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a), Asabe Madaki, Nafisat Abdullahi, Hadiza Gabon da Sidiqa Jibrin Sarki duk sun bayyana tasu yabawar a shafin na Ali Nuhu.
Zoben hanci daga: Leona Coco (@leona.coco_)Kwalliya daga: Beauty Glow (@beautyglow___)Gyale daga: Buccy Couture (@buccy_couture)Hoto daga: Talented DFK @talentedfk

![]()







