FITACCIYAR jaruma Fatima Abdullahi (Washa) ta je ƙasar Masar a makon nan domin hutu tare da yawon buɗe ido.
Jarumar ta wallafa wasu hotuna da ta ɗauka a can, inda aka gan ta a otal ɗin da ta sauka da kuma wuraren tarihi.

Washa ta je Sharm el-Sheikh, wani birni inda ake zuwa yawon buɗe ido. Birnin a bakin ruwa ya ke, tsakanin hamadar Tsibirin Sinai da Tekun Maliya.
A wannan gari akwai wuraren zuwa kallo sosai, musamman rairayi a bakin ruwa da gidajen cin abinci da kuma babban lambun ‘Ras Muhammad National Park’ inda ake zuwa miƙe ƙafa da kuma kurme.


Bugu da ƙari, Washa ta je garin Giza, wanda ke gaɓar Kogin Nayil daga yamma, kusa da Alƙahira, wato babban birnin ƙasar.
Babban wurin zuwa a garin shi ne Tsaunin Giza inda akwai ake kallon shirga-shirgan dala-dalar kaburburan sarakuna (fir’aunoni) na Masar ta dauri da shugabannin addini da manyan jami’an hukuma. An gina fitattun dala-dalar a ƙarni na 26 kafin haihuwar Annabi Isa (a.s.).
Dalar mafi girma ita ce wadda kabarin Sarki Khufu ya ke a ciki.


Ba wannan ba ne dai karon farko da Washa ta je ƙasar waje, domin kuwa har Ingila da Faransa da Dubai da Saudiyya ta je a shekarun baya.
Wasu fitattun jaruman Kannywood mata da su ka je yawon buɗe ido a Masar a baya sun haɗa da Ummi Zee-Zee, Rahama Sadau da kuma Nafisat Abdullahi.


Copyright © Fim Magazine
All rights reserved