A YAU, 26 ga Agusta, aka fara al’amuran Makon Hausa na Duniya.
A cikin 2015 ne aka fara gabatar da Ranar Hausa ta Duniya lokacin da wani ma’aikacin Sashen Hausa na BBC, Malam Abdulbaƙi Aliyu Jari, da wasu abokan sa na soshiyal midiya su ka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su haɗu su tattauna cigaba da kuma ƙalubalen da harshen ke fuskanta a ƙarni na 21.
A bara ne aka maida Ranar ta zama Makon Hausa, ganin cewa kwana ɗaya ya yi kaɗan a tattauna dukkan al’amuran kamar yadda ya kamata.
A kowace shekara idan ranar ta zagayo, ma’abota shafukan sada zumunta su na amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara.
Waɗanda su ka ƙirƙiro wannan maudu’in sun ce sun yi haka ne domin tunasar da al’ummar Hausa muhimmancin harshen da yadda za a ciyar da shi gaba.
Sannan kuma ranar ta kasance lokacin da ake ƙalubalantar Hausawa domin fiddo da sababbin bincike da nazarce-nazarce domin haɓaka harshen Hausa, misamman ta fuskar kimiyya.

Babbar nasarar da za a ce Ranar Hausa ta Duniya ta haifar ita ce haɗa kan al’ummar Hausawan duniya a duk inda su ke.
A cikin 2020, an gudanar da bikin Makon Hausa a ƙasashe 17, cikin su har da Faransa da Saudiyya.
Hausawa na haɗuwa a wannan lokaci domin sada zumunci da kuma tattaunawa a kan yadda za su taimaka wa juna.
Masana harshe da dama na yi wa Hausa kallon wani harshe mai yaɗuwa a faɗin duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ce harshe na 11 a faɗin duniya wajen yawan masu amfani da harshen, kuma shi ne na ɗaya a Afirka ta Yamma.
Sai dai akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin Swahili da ake yi a ƙasashe da dama na yankin Afirka ta Gabas ya ɗara Hausa da ake yi a yankin Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya yawan mutane masu amfani da shi.
Sai dai wasu nazarce-nazarcen sun nuna cewa Hausa na gaba da Swahili ta fannin yawan masu yin yaren, yayin da shi kuma Swahili ke gaba wajen yawan ƙasashen da ake yin yaren.
Tuni dai manyan kafafe irin su Facebook da Google su ke amfani da Hausa, kuma tuni manhajojin Android da IOS su ka shigar da shi cikin jerin harsunan da su ke amfani da su.
Ko a baya-bayan nan sai da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanya Hausa a cikin harsuna uku da ta zaɓa domin yaƙi da annobar korona a Afirka.
Ana fatan harshen Hausa zai samu karɓuwa nan ba da jimawa ba cikin harsunan amfani na Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Haɗa kan Ƙasashen Afirka (AU) da Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
Iyaka dai har yanzu ana buƙatar bincike sosai da nazari a kan harshen Hausa ta hanyar fito da sababbin ƙirƙire-ƙirƙire na zamani domin ɗaga martabar harshen.
Haka kuma ƙungiyar haɗakar ƙungiyoyin Hausawa na Afrika mai suna Gidauniyar Zumunci da ke da hedikwata a birnin Yamai ta sun ƙara wa bikin armashi ta hanyar fito da maudu’in makon na bana mai taken ‘Harshen Hausa Jiya Da Yau: Ƙalubale Da Hanyoyin Magance Su’, da su ka raba wa ƙungiyoyin Hausawa da ke Nijeriya, Kamaru, Sudan, Togo, Chadi, Senegal da kuma Gini Bissau.

Haka kuma ƙungiyoyi irin su Tsangayar Adabin Hausa da Dandalin Hausawan Kamaru da Facn da ke Jamhuriyar Nijar da sauran takwarorin su sun sanya gasa ga al’ummar gari don fito da manufofi da kyawawan al’adun malam Bahaushe.
Daga ƙarshe, fatan da masu shirya irin wannan taro da wannan mako su ke da shi shi ne buƙatar Hukumar Harsuna da Raya Al’adu ta Duniya (UNESCO) ta sanya wannan mako a cikin tabbataccen tarihi, ya kasance duk makon da ya kama daga ranar 26 ga Agusta ya zama makon da za a dinga gabatar da wannan biki da sunan Makon Hausa na Duniya a hukumance.
www.fimmagazine.com
Copyright © Fim Magazine. All Rights reserved