* Yayin da Al-Amin Ciroma ya yi murabus daga Farin Wata, Muhammad Iskeel ya bar Vision FM Katsina, ma’aikatan Vision FM Kano kuma sun yi shirin zuwa kotu
FITACCEN furodusa a Kannywood, Alhaji El-Sa’eed Yakubu Lere, ya maka shugaban hukumar daraktocin kamfanin rukunin gidajen rediyon Vision FM da gidan talbijin na Farin Wata a kotu, ya na neman ya biya shi naira miliyan 20 da ya ce ya na bi a lokacin da ya ke shugaban gidan rediyon a Kaduna.
Alhaji Umar Faruq Musa, Ciyaman ɗin kamfanin ‘Vision Media Services Limited’, ɗan asalin Jihar Kebbi ne kuma tsohon ma’aikacin Sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka (VOA).
Kamfanin, wanda hedikwatar sa ke Abuja, shi ne mamallakin tashoshin rediyon Vision FM a Abuja, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Gombe da Sokoto, da kuma tashar talbijin ta Farin Wata.
Yakubu Lere shi ne Janar Manaja na gidan rediyon Vision FM da ke Kaduna kafin a sallame shi kwanan baya.
Ya shigar da ƙara ne a Babbar Kotu ta 9 da ke NDA, Kaduna, inda ya ke buƙatar kamfanin ya biya shi naira miliyan 20 a matsayin diyya.
Kafin wannan ƙarar da ya shigar, Lere ya riga ya kai Umar Farouk Musa wasu kotuna biyu.
Ya shigar da ƙarar farko kan babban zargin ɓata suna da ƙazafi a kotun majistare da ke Titin Ibrahim Taiwo, Kaduna.
Ya ce maimakon wanda ake ƙarar ya kai kan sa kotun, sai ya garzaya wajen ‘yansanda da takardun binciken kuɗi na bogi da son rai, ya buƙace su da su binciki Leren.
Mujallar Fim ta ji daga wata majiya mai tushe cewa Umar ya kai Lere wajen ‘yansanda ne a kan zargin ya ɓatar da naira miliyan 10 na gidan rediyon a lokacin da ya ke riƙe da muƙamin Janar Manaja.
A ƙarar da ya shigar, Lere ya roƙi Babbar Kotu da ta hana ‘yansanda kiran sa, kuma ta umurci Umar ya biya shi naira miliyan 20 a matsayin kuɗaɗen da ya ke bin kamfanin.
Kotun ta sanya ranar 23 ga wannan watan na Nuwamba domin fara sauraren ƙarar.
Ɗaya ƙarar da Lere ya maka Umar Farouk Musa, ya shigar da ita ne a Kotun Ma’aikata ta Ƙasa (National Industrial Court) da ke Kaduna, ya na so ya biya shi wasu kuɗaɗe da su ka haura naira miliyan 4.

A wannan ƙarar, Lere ya yi iƙirarin cewa shugaban kamfanin na Vision ya yaudare shi lokacin da ya naɗa shi Janar Manajan tashar rediyon, inda ya ba shi tabbacin cewa za a tanadar masa dukkan abin da ya ke buƙata domin cimma nasara, to amma sai da ya zurma kan sa sai ya faɗa masa cewa kamfanin ba ya da kuɗin da za a fara aiki da kuma na gudanarwa.
Lere ya faɗa wa kotun cewa haka aka bar shi ya yi ta haƙilon neman kuɗin man injinan janareto biyu da ke tashar da sauran kuɗaɗen gudanarwa.
Bugu da ƙari, ya ce an buƙace shi a tsakanin watannin Oktoba zuwa Disamba na 2021 da ya ɗau ma’aikata ya horas da su, ya ƙirƙiro shirye-shirye da abin da za a saka a cikin su a bisa yarjejeniyar cewa za a biya shi dukkan kuɗaɗen da ya kashe daga bisani, amma sai ciyaman ɗin ya karya alƙawari.
A takardar ƙarar mai shafi biyar, Lere ya kuma faɗa wa kotun cewa an yanke masa rabin albashi har na tsawon watanni 18 ba bisa ƙa’ida ba, kuma an ƙi biyan sa kamasho da kuɗin aljihun sa da ya kashe waɗanda sun haura naira miliyan biyu.
Lere ya ƙara da cewa bayan ya dinga tunatar da ciyaman ɗin batun waɗannan kuɗaɗe nasa, maimakon ya biya shi sai kawai ya turo masa wani mai binciken kuɗi wanda bai da takardar shaidar cancanta, ya ce wai ya bincike shi da nufin a kama shi da laifi.
A cewar sa, a ƙarshe mai binciken kuɗin ya miƙa rahoto inda ya nuna ya kama Lere da laifi, kuma ya bada shawarar a kore shi daga aiki, kuma ciyaman ɗin ya amince ba tare da ya bi ƙa’idar yin hakan ba.
Lere ya ce saboda waɗannan abubuwan, ya na so kotun ta umarci shugaban kamfanin da ya biya shi dukkan kuɗaɗen sa sannan ya gyara korar da ya yi masa ba bisa ƙa’ida ba.
Kotun dai ta saka ranar 2 ga Disamba, 2021 domin fara sauraren wannan ƙarar.
Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa bambancin siyasa ne ummulhaba’isin saɓanin da aka samu tsakanin Lere da masu kamfanin ‘Vision Media’, waɗanda wasu tsofaffin ‘yan jarida ne da ‘yan kasuwa.
Majiyar ta ce, “A yayin da Yakubu Lere ba ya ɓoye goyon bayan sa ga jam’iyyar PDP, su kuma masu Vision ‘yan APC ne. Sau da yawa sun riƙa hana Lere yaɗa shiri da ya shafi kyautata wa PDP a tashar ko wanda ya ɗan taɓa mutuncin jam’iyyar APC.”
Majiyar ta ce Umar ya sha yi wa Lere ƙofar-raggo domin ya samu damar kama shi da laifin da zai sa ya bar kamfanin ko ta halin ƙaƙa.
Wakilin mu ya gano cewa ban da Lere, su ma wasu manyan ma’aikatan na Vision Media sun fuskanci matsala da kamfanin.
Cikin su har da Janar Manaja na tashar rediyon Vision FM da ke Katsina, Alhaji Muhammad Iskeel, da Janar Manaja na gidan talbijin ɗin Farin Wata, Alhaji Al-Amin Ciroma, da kuma shugabannin gidan rediyon Vision FM da ke Kano.
Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta shaida wa wakilin mu cewa Iskeel, wanda shi ne Janar Manajan tashar a Katsina na huɗu da aka naɗa cikin shekaru biyar (wanda kuma ya fi sauran daɗewa), ya aje aikin saboda arangamar da ya sha yi da mahukuntan kamfanin.
Majiyar ta ce babbar matsalar da ya fara samu tsakanin sa da su ita ce: “‘Rate’ ɗin Vision ta kwata 1 shi ne N650,000; sai ya sami N1.2m, sai ya riƙa ba su N750,000. Daga baya da su ka ji sai su ka ce sai ya bada cikon.
“Sannan direban shi ya fita da mota aka sace a hannun shi. Aka ce sai ya biya. An riƙe masa albashi na tsawon wata takwas, kuma an hana shi kamashon N900,000.”
A yanzu dai Iskeel, wanda shi ma babban furodusan finafinan Hausa ne, ya samu wani aikin, an naɗa shi Janar Manaja na tashar rediyo ta Liberty FM a Kano.
Shi ma Al-Amin Ciroma, wanda tsohon Editan jaridar ‘Leadership Hausa’ ne, ya aje aiki a cikin watan Satumba da ya gabata ne saboda wasu matsaloli da aka kasa warwarewa.
Majiyar ta ce, “Ciroma ya nemi a yi ‘reassigning’ ɗin shi daga Manaja zuwa harkar kasuwanci don ya samu lokacin wasu harkokin sa. Na biyu, ya nemi a cire shi daga tsarin albashi, illa iyaka idan ya samo wata harka ta kuɗi, to a ba shi kason kamasho mai tsoka (30%), kuma aka amince.”
Amma duk da yake ya bar aikin, Ciroma ya na gabatar da wasu shirye-shirye da ya ke yi a baya; shi ya sa ake ganin kamar bai bar tashar ba.
Ciroma dai shi ne Kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Mashirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), kuma shi ne mijin Hajiya Wasila Isma’il, jarumar fitaccen fim ɗin da Yakubu Lere ya yi suna da shi, wato ‘Wasila’.
A tashar rediyon Vision FM da ke Kano kuwa, aƙalla manyan ma’aikata 12 su ka aje aiki tare da yi wa kamfanin barazanar za su kai maganar kotu don a bi masu haƙƙin su, musamman tarin albashi da aka hana su.
Mujallar Fim ta ga kwafe ɗin takardar koke da ma’aikatan su ka rubuta, su na neman a biya su albashi da alawus ɗin su da ya kama N8,502,420.
A takardar, mai ɗauke da kwanan wata 29 ga Oktoba, 2021, wadda lauyan su, B.A. Mu’az na cambar ‘H.H. Ma’aruf & Co.’ ya aika wa shugaban kamfanin, ma’aikatan sun bada wa’adin kwana bakwai a biya su ko su kai ƙara kotu.
Tun a cikin watan Mayu na bana ne ma’aikatan su ka aje aiki.
Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa an maye gurbin su da wasu ma’aikatan, “amma duk ba ta sake zani ba”.

A takardar aje aiki da su ka aika wa Alhaji Umar Farouk Musa a ƙarƙashin jagoran su, Janar Manaja na Vision FM Kano na lokacin, Alhaji Adamu Ladan, ma’aikatan sun ce an ɗauke su aiki ne bisa wa’adin gwaji na wata shida a watan Janairu 2019, to amma har aka samu shekara biyu ba a biya su ba.
Tsofaffin ma’aikatan su ka ce sun yi wa shugaban kamfani tuni sau tari, amma ba su samu biyan buƙata ba.
A takardar koken su, sun yi kira ga kamfanin da ya biya su albashin su da sauran kuɗaɗen su.
Ma’aikatan da su ka aje aikin sun haɗa da Adamu Salihu Ladan, Muhammad Garba, Ahmad Rufa’i Bello, Kyaftin Abdullahi Adamu Bakoji (ritaya), Sadik Muhammad Kiyawa, Aliyu Abubakar Getso da Mustapha Khamis.Sauran su ne Ashiru Shehu Kachako, Isyaku Turaki Maje, Lami Sumayya Murtala, Samira Adam da Lami Shema, da sauran su.Ma’aikatan sun tura kwafen takardar koken su zuwa ga hukumomin ‘yansanda, EFCC, da DSS da ke Kano.
![]()







