• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jami’ar Jihar Sokoto ta shirya gasar rubuta ‘waƙa kwaikwaye’

by DAGA IRO MAMMAN
October 25, 2021
in Marubuta
0
Ƙofar Jami'ar Jihar Sokoto

Ƙofar Jami'ar Jihar Sokoto

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SASHEN Koyar Da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Jihar Sokoto ya shirya gasar rubuta wani salon waƙar baka ko rubutacciya da ya kira “waƙa kwaikwaye”.

A takardar bayanin gasar wadda mujallar Fim ta samu, an bayyana ‘waƙa kwaikwaye’ da “waƙar da ta ƙunshi hira ko musanyar magana tsakanin mutane biyu ko fiye.”

An ci gaba da bayyana cewa a irin wannan waƙa mai saurare ko karatu zai iya ganin mutanen cikin zuciyar sa, “kamar ya na kallon wasan kwaikwayo.”

Masu shirya gasar sun bada misalin irin wannan waƙar kamar haka: “A waƙoƙin baka na Kassu Zurmi ko Gambo ko Shata ko Ɗanƙwairo duk akwai irin wannan tsari.

“A waƙar Shayi wadda Kassu ya yi akwai inda iyayen ‘yan mata su ke tambayar Kassu da ya ba su labari game da Shayi wanda ‘ya’yan su su ke so ya aure su.”

A cewar jami’ar, a rubutattun waƙoƙi ma a kan samu irin wannan. Misali ita ce waƙar ‘Karuwa’ wadda Mu’azu Haɗejia ya rubuta, “don akwai inda karuwa da manemin ta su ke musayar magana, ita ta yi cikin fushi, shi kuma ya na lallashin ta.”

Hatimin Jami’ar Jihar Sokoto

Mashirya gasar sun kuma bayyana cewa take ko maudu’in gasar shi ne “Matsalar Taɓarɓarewar Tarbiyya da ta Rashin Tsaro a Arewacin Nijeriya.” A kan wannan ne duk mai son shiga gasar zai shirya waƙar sa.

Ƙa’idojin shiga gasar bakwai ne, kamar haka:

1. Tilas ne waƙa ta sa mai sauraro ya ji cewa mutane biyu ne ko fiye, amma kada su wuce uku, su ke yin hira.

2. A sanya waƙar a kan takarda ko cikin odiyo ko bidiyo (a kan faifan sidi idan da hannu za a kawo) sannan a aiko ga adireshin da aka bayar.

3. Tilas mawaƙi da masu rera waƙa cikin bidiyo su kasance cikin sutura ta mutunci a al’adun Hausawa.

4. Tilas ne mai rubutacciyar waƙa shi zai rera waƙar sa da kan sa, ko ya kasance ya na nan a wurin gasar tare da wani da ya sa ya rera masa saboda wata lalura.

5. Ana so marubucin waƙa ya zo wurin taron shi kaɗai ba tare da ‘yan amshin sa ko waɗanda su ka taya shi rera waƙar sa ba, saboda su na cikin odiyo ko bidiyon da ya riga ya aiko domin kuwa kwamitin gasar ba zai ɗauki nauyin su ba idan su ka zo tare.

6. Ana buƙatar kada waƙar baka ta gaza kai ɗiya 30, kuma kada ta wuce 35; rubutattar waƙa kuma kada ta kasa baitoci 40, kar kuma ta wuce 45, kowane baiti ya kasance mai ɗango 5, wato ƙwar 5.

7. Mawaƙi ya haɗo da taƙaitaccen tarihin sa a rubuce.

Bayan haka, akwai abubuwan da aka haramta wajen shiga gasar, kamar haka:

1. Kada a kama sunan wani ko na wata ƙabila ko na wata hukuma ko na jinsi ko na wani ɓangare.

2. Kada a yi batsa a cikin waƙa.

3. Kada a kushe kyawawan al’adun Hausawa ko a ɗaukaka al’adun wasu al’ummomi a kan na Hausawa.

Za a karɓi saƙonnin masu son shiga gasar a tsakanin ranar 1-14 ga Nuwamba, 2021, sannan za a bayyana sakamakon gasar a ranar 15 ga Disamba, 2021.

Za a faɗi ranar da za a yi bikin karrama zakarun gasar daga baya.

An buƙaci masu son shiga gasar da su aika da waƙar su ta wannan adireshin na imel: gwkwaikwayessu21@gmail.com ko ta hannun Dakta Aliyah Adamu Ahmad.

Haka kuma an bada lambobin waya saboda masu so su kira don samun ƙarin bayani kamar haka: 08133314217 da 08095059926.

Loading

Tags: Adabin HausaAliyah Adamu Ahmadgasar rubutuHausaJami'ar Jihar SokotoMu'azu Hadejiarubutacciyar wakaSashen Koyar Da Harsunan NijeriyaShayi Dan Gidan LabboSokoto State Universitywaka kwaikwayewakar bakawakar Hausa
Previous Post

‘Yan sanda na binciken yadda jarumi ya harbe mai shirya fim da bindiga a lokeshin

Next Post

Cewar Afakallah: Na yafe wa Aliyu Sabo Bakin-Zuwo cin mutunci na da ya yi, to amma…

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Cikin gajeren bidiyo, Aliyu Sabo Bakin-Zuwo (a hagu) ya nemi afuwar Isma'il Afakallah (a dama)

Cewar Afakallah: Na yafe wa Aliyu Sabo Bakin-Zuwo cin mutunci na da ya yi, to amma...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!