INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Yanzun nan labari ya ɓullo cewa Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumin Kannywood Umar Gombe rasuwa a yau.
An shaida wa mujallar Fim cewa Alhaji Sani Labaran ya rasu ne ɗazun nan a garin Gombe bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Ba mu samu cikakken bayani ba, amma wata ƙwaƙƙwarar majiya ta ce za a yi jana’izar sa gobe da ƙarfe 10 na safe a fadar Sarkin Gombe da ke Gombe.
Allah ya rahamshe shi, ya ba iyalin sa haƙurin wannan babban rashi, amin.
![]()







