• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shekara 8 da aure: Mijin Fati Ladan, Yerima Shettima, ya wallafa hotunan murna

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 21, 2021
in Ranar Murna
1
Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello (a tsakiya), tare da Yerima Shettima da amaryar sa Fati Ladan a lokacin da gwamnan ya ziyarci gidan su

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello (a tsakiya), tare da Yerima Shettima da amaryar sa Fati Ladan a lokacin da gwamnan ya ziyarci gidan su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A JIYA Litinin, 20 ga Disamba, 2021 tsohuwar fitacciyar jaruma Fati Ladan da mijin ta, fitaccen ɗan gwagwarmaya kuma shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum), Alhaji Yerima Shettima, su ka cika shekara takwas cur da aure.

Da misalin ƙarfe 6:23 na yammacin jiya Yerima Shettima ya fara ɗora hotunan su a WhatsApp Status ɗin sa da kuma shafin sa na Instagram don nuna farin cikin sa game da wannan rana mai ɗimbin tarihi a gare su.

A ƙasan ɗaya daga cikin hotunan, Yerima ya rubuta: “Happy 8th wedding anniversary my princess”.

 

Haka kuma a shafin sa na Instagram ya ɗora hoton su da Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a ranar da ya ziyarci gidan sa da ke Jinya Close, Kanta Road, Kaduna. A ƙasan hoton ya rubuta, “Happy wedding anniversary my princess, and also @ Governor Yahaya Bello of Kogi state, thanks for dis wonderful visit to my home and families. God bless u.”

Haƙiƙa, Fati Ladan ta na ɗaya daga cikin jarumai mata da su ka yi aure su ka ba maraɗa kunya. 

Sanin kowa ne an fi sa ido kan mutuwar auren matan Kannywood, duk da yake matsala ce da ta addabi Arewa.

A wata hira da mujallar Fim ta taɓa yi da jarumar a shekarar 2019, bayan haihuwar ‘yar ta Humaira, mun tambayi Fati cewa, “An ce idan ‘yar fim ta yi aure ana yi mata zarya, wasu daga cikin masu zuwa su na zuga ta ne don ta fita, wasu kuma masu zuwa su na ƙara mata ƙarfin gwiwa ne don ta zauna. Idan har kin fuskanci irin wannan ƙalubalen, wane abu ki ka ɗauka wanda ya jawo maki sirrin zaman ki har yanzu?”

Sai ta ce, “Katanga. Ka san Hausawa sun ce sai bango ya tsage ƙadangare ke samu ya shiga. 

“Ni babban nasara na a zaman aure na gaskiya katanga na yi, ban bada ƙofa ga irin waɗannan mutanen su shigo gida na ba. Don haka katangan da na yi da kuma taimakon Allah ya sa na samu nasara.”

Sai wakilin mu ya ce mata: “Idan ki ka ce katanga, ya na nufin kenan kin ƙaurace wa abokan sana’ar ki da ku ka yi harkar fim tare kenan?” 

Sai ta amsa: “Abokan sana’a na mu na mu’amala. Babu kuma abin da ya canza. Idan na ce katanga, ba ina nufin ‘yan fim ɗin mu kaɗai ba. Ai su masu hana ruwa gudu ba a cikin harkar fim ɗin kawai su ke ba, ko a ina za ka iya haɗuwa da su, maƙwabtan ka ne ko abokan zaman ka ne, ko’ina ka na tare da su. Don haka in ka ce ka yi katanga, ba wai ka na nufin mutanen da ka ke sana’a ba ne da su kawai. 

“Kowa ya na da matsala; katangan da ka yi ka killace kan ka daga irin waɗannan tsirarun mutanen da su ke so su hana maka ruwa gudu a cikin zamantakewar auren ka.”

Wannan shi ne sirrin zaman Fati Ladan a gidan mijin ta. Kuma kowa ya na ganin yadda mijin nata ke nuna mata ƙauna a kowane lokaci duk da ba ita kaɗai ba ce matar sa.

Allah ya ƙara zaunar da su lafiya tare da fatan ƙara samun haɗin kai a tsakanin su.

Da kuma fatan sauran matan Kannywood da ma sauran matan da ba ‘yan fim ba za su ɗauki irin salon da Fati Ladan ta ɗauka a yayin zaman auren ta.

Loading

Tags: aureFati LadanGovernor Yahaya BelloWedding AnniversaryYerima Shettima
Previous Post

Aure ya sa na fara ganin kyakkyawan sauyin rayuwa, inji mawaƙi Abdul D. One

Next Post

Hotuna: Fati Ladan da Yerima Shettima sun cika shekara 8 da aure

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Hotuna: Fati Ladan da Yerima Shettima sun cika shekara 8 da aure

Hotuna: Fati Ladan da Yerima Shettima sun cika shekara 8 da aure

Comments 1

  1. Pingback: فاتي لادان تحصل على ولد جديد وتفرح

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!