JIRAN da aka daɗe ana yi na ganin auren fitaccen furodusa Abubakar Bashir Maishadda da fitacciyar jaruma Hassana Muhammad ya zo ƙarshe, domin kuwa a watan gobe ne za a ɗaura auren su.
Za a ɗaura auren nasu da misalin ƙarfe 11:00 na safe a ranar Lahadi, 13 ga Maris, 2022 a Masallacin Murtala da ke Kano.
Da farko, sai da Maishadda ya yi ɓadda-bami inda ya wallafa wasu hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) masu nuna shi tare da jaruma A’isha Ahmad Idris (A’ishatul Humaira) a shafin sa na Instagram, wanda ita ma Humairar ta raba a shafin ta.

Ashe dai ba a nan gizo ke saƙar ba, domin kuwa furodusan ya shirya tsaf don angwancewa da santaleliyar sabibar sa, Hassana, wadda labarin soyayyar su ba ɓoyayye ba ne.
Abubakar da Hassana sun kai aƙalla shekara biyar su na soyayya.
Daga baya an daina ganin jarumar a cikin finafinai, wanda ake kyautata zaton saurayin nata ne ya hana ta.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa a mako mai zuwa furodusan zai fitar da hotunan kafin aure nasa da Hassana.
Ah ya badda-bami kam😄. To sai once Allah ya sanya alheri ya kai mu lokacin aminn🤲