• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 10, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Bugu Da Guduma

by DAGA IBRAHIM SHEME
August 26, 2012
in Marubuta
0
Malam Ibrahim Sheme

Malam Ibrahim Sheme

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Allah na, ya sarki gwani,
Roƙo na ka yi zan soma.

Buɗe mini tagar zurfafa-
War ƙwalwa, ban ilhama.

Domin manzon ka Ahmadu,
Wannan ɗan hannun dama.

Don Dija uwar duka muminai,
Don Zainab bint Khuzaima.

Wannan matan na Muhammadu,
Ar-Rasul hannun sa na kama.

Wani ja’iru ɗan ɗan karuwai,
Shi ne ya taɓo ne da kima.

Wai ya riƙe gurnati har da bam,
To gu nai ba ni da girma.

Shawaraki zo zauna ka ji,
Koli na za ni baje ma.

Ka ɗauka na manta da kai?
Ho takari da babu igama!

Yau sam sam lallai ba ragi,
Wallai ni sai na rama.

Dundu da gula zan yi maka,
Ga ƙusa za ni buga ma.

Kai tashi da mugun gyangyaɗi, 
Sabon saƙo zan yi ma. 

Yasin ce zan jawo maka,
Alƙunut kai har ma Amma.

Ko ko dai baiti ’yan kaɗan,
Babban gyambo in fama?

Ɓarawo ne na ƙwaƙwalwa, 
Nomau ɗan Sarkin Noma!

A kwatar can nats tsamo ka,
Wawan kai sai kak koma.

Na ba ka kuɗi har fam ɗari
Jari, ga shanun noma.

Su ne ka kaɗar ga kilakilai,
Ka koma dogon hamma.

Kullum zagin mu cikin gari,
Harshe ya kai mil goma.

Kullum sara ta ɗai ka ke,
Ni gamji ina daɗa girma.

To ganye ne ka ka sassabe,
Ni tushe na bai suma.

Na gode Allah Rahimi,
Duniyar nan na sha fama.

Yau ga ni garas kuma tangaran,
Ƙarfi ma yanzu na soma.

Farkar ka a rannan ta dafa
Maka girki, oh tai himma!

Ta ba ka tuwo ka nannaga,
Wulli mai babbar loma.

Soyen alade ta buga maka,
Ta ba ka da dambun nama.

Ka take cikin ka da burkutu,
Ka ɗauka koko ta dama!

Sarkin kwaɗayi, mai kwarmato,
Doki mai ƙarnin nama.

Kai ba ka aboki yanzu mai
Sallah, sai arnan Koma.

Wawan sarki ba ka da kai, 
Ɓutal, gyandai, camama. 

Sannun ka da ƙaryar arziƙi, 
Banza kullum sai homa. 

Bayahude lallai ka riƙa,
Wai kai yau babu hukuma.

Dolo har yau ba ka kintsu ba,
Kai kullum ka sha mama.

Bunsuru mai neman ’ya tasa,
Domin kai ba ka iƙama.

Mai danne yara ƙanƙana,
Da uwar ma in ka ga dama.

Ba jinƙai, mugun makiri?
Ka zambaci hatta umma.

Mai laifi ba ka da karsashi,
Ɗan sanda kai yak kama.

Kai tusa, warin ya bugo 
Daga Legas ya kai Bama. 

Izzar ka ta ja maka zunguri,
Ga tarko na ya kama.

Je tuba ka daina haɗin faɗa,
In ka ƙi mu dinga husuma.

Yaƙin biro kuma ni da kai,
To yanzu ka san na soma.

Sunan ka mance? Iro ne,
Ko ‘Sheme bugu da guduma’.

Mai horon arna jiddadum,
To yau dai kan ka na koma.

Dangi na ku na gaida ku,
Addu’a a gare ku na nema.

Aikin da na ke kun taimaka,
Hannu kun sa kun tama.

Ƙyale ni na harbi haƙarƙarin
Mugu mai sato nama.

Zan karya wuyan azzalumi,
Kun san ni da zafin nama.

Ƙarshe nan ni roƙo na yi,
Ya Jallah ka ba ni in kama,

Igiyar nan ta Islamiyya,
Na tuba gare ka na koma.

Baitin waƙar mu guda biyar,
Sai ku tara har sau goma.

TAMAT

Ibrahim Sheme
Agusta, 2012

Loading

Tags: adawabugugudumaIbrahim ShemekaruwaishaguɓeWaƙezambo
Previous Post

‘Ahayye Ya Ahayye’

Next Post

Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

Waƙar 'Musa Na Ƙasar Ɗan'ali' ta Kassu Zurmi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!