• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

A harkar fim na samu kuɗin buɗe katafaren shagon sayar da tufafi – Maishadda

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 2, 2022
in Labarai
3
Abubakar Bashir Maishadda a wajen taron

Abubakar Bashir Maishadda a wajen taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN furodusa a Kannywood, Alhaji Abubakar Bashir Maishadda, ya bayyana cewa daga harkar fim ne ya samo kuɗin da ya buɗe katafaren shagon nan na sayar da tufafi da ya ƙaddamar a ranar Juma’a, don haka ba harka ce da zai yi wasa da ita ba.

Ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Harkar fim ita ce ni, ka ga kuwa in babu ita babu ni. Ko kuɗin da na buɗe shago, ai da fim na same su. Fim ba sana’ar da zan bari ba ne.”

An yi bikin buɗe shagon mai suna ‘Mai Shadda Textile’ a ranar Juma’a, 30 ga Satumba, 2022, wato shago mai lamba 5 da ke MYCA 7, Plaza, a Titin Gidan Zu, a Kano.

A yayin da ya ke tattaunawa da wakilin mu, Maishadda ya bayyana matuƙar farin ciki, ya ce: “Alhamdu lillah. Babu abin da zan ce wa Allah (s.w.t.) sai dai in gode masa. Na kuma yi farin ciki sosai da Allah ya nuna mani wannan lokaci. 

Ɗimbin mahalarta taron su na shiga shagon

“Kasancewar da ma irin wannan sana’ar mu na yin ta a ɓoye, wannan karon sai mu ka ga ya kamata mu bayyana shi saboda mutane su sani, saboda duk wani abu da ake nema na ɓangaren yaduddika, shaddodi, jakunkuna, takalma, duk mu na da su.

“Kuma in-sha Allahu za mu riƙa ba da farashi irin yadda ake ba da wa a kasuwa. Zai zamana da ka shiga cikin kasuwa ka haɗu da gosulo ran ka ya ɓaci, gwanda ka zo wurin mu ka saya.”

Dangane da yadda zai iya haɗa wannan kasuwancin da sana’ar fim kuwa, furodusan ya ce ai yayar sa da ƙanwar sa ne zai bar wa aikin gudanar da shagon yayin da shi kuma zai ci gaba da harkar sa ta fim.

Ya ce: “Ai wancan kasuwancin ba ni ne a kai ba, yaya ta ce da ƙanwa ta su ke kula da shagon. 

“Harkar fim kuma harka ta ce da na ke kan yin ta. Harkar fim ita ce ni, ka ga kuwa in babu ita babu ni. Ko kuɗin da na buɗe shago, ai da fim na same su. Fim ba sana’ar da zan bari ba ne. Har gobe ina ci gaba da yi.”

Mawaƙin siyasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), shi ne uban taro a bikin ƙaddamarwar, wato shi ne ya jagoranci buɗe shagon.

Ɗimbin ‘yan fim da su ka halarci taron sun haɗa da Adam A. Zango, Daddy Hikima, Nura M. Inuwa, Yakubu Muhammad, El-Mu’az Birniwa, Umar Gombe, Rasheeda Adamu Abdullahi, Sadiq Zazzaɓi, Hafizu Bello, Aisha Ahmad Idris (Aishatulhumaira), da Abba Miko Yakasai, Mustapha Nabraska, Siddiqa J. Sarki, da sauran su.

Rarara da Maishadda tare da su Daddy Hikima, Nura M. Inuwa da Adam Zango za su yanka zaren ƙaddamar da shagon

Ita ma matar Maishadda, tsohuwar jaruma Hassana Muhammad, ta halarci taron tare da ‘yan’uwan su na jini.

Tun wajen ƙarfe 3:00 na rana aka fara taron, amma ba a tashi ba sai wajen ƙarfe 10:00 na dare saboda cincirindon mutane.

Rarara da Daddy Hikima su na raha da Adam A. Zango
‘Yan’uwan Abubakar Maishadda a wajen taron
Ayshatulhumaira (a hagu) da Rashida Adamu Abdullahi a taron

Loading

Tags: Abubakar Bashir MaishaddaDauda Kahutu RararaHassana MuhammadKannywoodkasuwanciMai shadda Textileshagon tufafiTaro
Previous Post

Ba ruwa na da kamfen ɗin Tinubu, inji Rahama Sadau

Next Post

Safzor ya samu ƙaruwa da Amal

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Saifullah (Safzor) da Amina (Amal)

Safzor ya samu ƙaruwa da Amal

Comments 3

  1. Pingback: A harkar fim na sami kudaden dana bude katafaren shagon saida kowane irin tufafi don haka bazan bar harkar fim ba, cewar Abubakar Maishadda - Kyauta Blog
  2. Pingback: Yadda aka gudanar da shagalin bikin bude katafaren shagon tufafi na Abubakar bashir Mai shaddah - Dailygistnaija
  3. Pingback: A harkar fim na samu kuɗin buɗe katafaren shagon sayar da tufafi – Maishadda - LastNg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!