ALLAH ya azurta daraktan finafinai a Kannywood, Malam Saifullah Isyaku Idris, wanda aka fi sani da Safzor, da santaleliyar ‘ya mace.
Matar sa, Khadija, ta haihu a ranar Asabar, 1 ga Oktoba, 2022 da misalin ƙarfe 11:30 na dare a wani asibiti mai suna Al-Munir da ke kusa da unguwar NDA a Kaduna.
Kamar yadda a yanzu ba a jira sai ranar suna ake bayyana sunan jariri, su ma sun raɗa wa ‘yar tasu suna Amina, amma su na kiran ta da Minal.
A ranar mai zuwa za a yi taron suna in Allah ya kai mu.
Allah ya raya Amal bisa tafarkin Manzo (s.a.w.), ya albarkaci rayuwar ta, amin.
![]()







Comments 1