KAMAR yadda ta saba yi a kowace shekara, a bana ma jarumar Kannywood Saratu Gidado (Daso) ta ci gaba da rabon abincin buɗa-baki ga yara a gidan ta.
A kullum Hajiya Saratu na ciyar da yara da ke cika a gidan ta da ke Unguwar Chiranci a cikin Birnin Kano.
A wajen rabon abincin, kamar yadda wakilin mujallar Fim ya gani a jiya Juma’a, ana raba dafaffiyar shinkafa da taliya da doya da naman kaji da na shanu da kuma kayan marmari.
Da mujallar Fim ta tambaye ta dalilin wannan ciyarwar da ta ke yi da azumi, sai Daso ta ce: “To, ita wannan ciyarwar da man ina yin ta duk ranar Juma’a. Na kan tara yara na raba musu abinci sadaka, amma da azumi kullum na ke fadawa na raba, kuma haka na ke yi duk shekara.”
A game da maganar da ake yi na cewar ciyarwar da ta ke yi iya yara ne kuwa, cewa ta yi, “To gaskiya ni ciyarwar da na fi mayar da hankali a kan ta ita ce ta marayu da kuma almajirai, don haka aka fi ganin yara a wajen rabon abincin da na ke yi.

“Su marayu da almajirai su ne su ka fi zama abin tausayi, shi ya sa na fi mayar da hankali a kan su. Amma su ma manyan mu na raba musu, don mu na ɗaukar kayan abinci mu shiga ƙauyuka domin raba wa mabuƙata.”
Da mu ka tambaye ta ko akwai bambanci tsakanin wannan shekarar da bara, sai ta ce, “Gaskiya akwai bambanci, domin a shekarar da ta gabata mun fi samun tallafi daga wajen mutane da su ke bayar da gudunmawar kayan abincin da mu ke rabawa, amma a bana ko don yanayin da ake ciki ne ya sa ba mu samu ba. Wannan shekarar gaskiya akwai ƙarancin abubuwan da mu ke samu na gudunmawa don rabawa ga jama’a. Amma dai har yanzu ƙofar mu a buɗe ta ke ga duk wanda ya ke son ya bayar da tasa gudunmawar domin ciyar da masu buƙatar da mu ke da su, don su na da yawa a cikin al’umma. Fatan mu dai Allah ya haɗa mu a ladar.”