• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin takaici ne da ‘yan Kannywood su ka ƙaurace wa taron KILAF – Sani Mu’azu

Wuri ne na kwasar ilimi, inji shi

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 27, 2023
in Labarai
0
Abin takaici ne da ‘yan Kannywood su ka ƙaurace wa taron KILAF – Sani Mu’azu

Alhaji Sani Mu'azu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON Shugaban Ƙungiyar Ƙwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Alhaji Sani Mu’azu, ya bayyana takaici kan rashin halartar ‘yan Kannywood tarurrukan da aka gudanar na tsawon kwanaki ana koyar da harkokin kasuwanci da kuma sana’ar fim, wato Biki Da Baje-kolin Finafinan Harsunan Gadon Afrika na Kano (KILAF) duk da yake a cikin garin Kano aka yi shi kuma nan ne cibiyar harkar finafinan Hausa.

Alhaji Sani, wanda fitaccen jarumi ne a masana’antar, ya bayyana hakan ne ga mujallar Fim jim kaɗan bayan kammala taron a jiya.

A lokacin da mu ka nemi jin ra’ayin sa kan yadda taron ya gudana, sai ya ce: “To alhamdu lillah, taro dai an yi shi lafiya kuma ga shi mun zo ƙarshen sa lafiya.

“Taro ne na ƙara wa juna sani, kuma mu da aka gayyata a matsayin waɗanda za mu bada jawabi ko kuma mu ka gabatar da laccoci a wannan waje, mun yi ƙoƙari mun koyar da abubuwan da su ka shafi aktin da ‘yan wasa su ke yi.

“Kuma mun yi ƙoƙari wajen fito da ƙa’idoji ko kuma tsare-tsare na abubuwan da ya kamata mutum ya sani da ya kamata ya yi da kuma wanda bai kamata ya yi ba a matsayin sa na jarumi ko jaruma.

“Mun yi ƙoƙari mu nuna wa mutane cewa a cikin wannan aikin da mu ke yi ba wai aiki ne na wasa ko na sharholiya ba. Aiki ne da yake da ƙa’ida da dokoki. Kuma mun lissafa wa mutane irin waɗannan dokokin don su gane cewa in ka na cikin aikin ba za ka iya sakin jiki cewa ka yi yadda ka ke so ba. Lallai ne sai ka gane cewa akwai ƙa’ida a matakin abin da za ka yi, musamman a mu’amala tsakanin ka da jama’a da kuma sauran abokan aikin ka da kuma kai kan ka.

“Don haka lallai dole mutum ya san irin waɗannan dokokin don ya san irin yadda zai gudanar da sana’ar sa.”

Dangane da ƙarancin zuwan ‘yan Kannywood a taron, jagoran ya ce: “To, gaskiya abin takaici ne ka ga waɗansu sun taso tun daga Zimbabwe sun zo wannan wajen don su halarci taron, wasu sun tsallako kan iyaka daga Nijar sun shigo don su halarta, wasu sun taso daga Legas sun zo. Amma a ce kai ka na Kano kuma aikin da ka ke yi kenan, aikin da ka ke yin tutiyar shi ne, aka san ka a kai, amma ka kasa zuwa ka halarci wannan taron. Don haka gaskiya wannan abin takaici ne.”

Sani Mu’azu ya yi kira ga ‘yan fim da cewa: “Kiran da zan yi shi ne duk wanda da gaske halastaccen ɗan wannan masana’anta ne ya gane cewa ba za ka iya yi ba tare da ilimi ba, don haka in ka samu dama wadda za ka ƙara ilimi to kada ka yi wasa da ita, ka zo ka yi ƙoƙari ilimin naka ya ƙaru saboda a yadda ka ke gudanar da ayyukan ma za ka ga ka samu cigaba ka yi shi daban, ba kamar wanda ya ke yi a cikin jahilci ba.

“Domin kuwa shi wannan taron ita masana’antar za ta ci gajiyar sa da ilimi, don babu shakka an bayar da ƙasidoji daban-daban waɗanda a fannoni na ilimi da aka zo da su kuma an samu damar haɗuwa da wasu mutane na wasu wurare. Ka ga an samu damar da ayyukan mu za su kai ga wasu wurare wanda a baya ba ma tunanin za su iya kaiwa.

“Sannan za a ɗabbaka waɗannan abubuwan da mu ka yi a buga littafin wanda za a tara ilimin, wanda ‘yan baya ma za su zo su yi amfani da abubuwan da aka koyar. Don haka ya na ɗaya daga cikin abubuwan da aka samu a cikin wannan taro.”

Loading

Tags: KannywoodKILAF 2023Sani Mu'azu
Previous Post

‘Ngoda’, fim daga Zimbabwe, ya wawashe kyaututtukan gasar KILAF 2023

Next Post

Furodusa Abdul Amart ya saya wa iyalan darakta Aminu Bono gida, Rarara kuma ya ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan marigayin

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Furodusa Abdul Amart ya saya wa iyalan darakta Aminu Bono gida, Rarara kuma ya ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan marigayin

Furodusa Abdul Amart ya saya wa iyalan darakta Aminu Bono gida, Rarara kuma ya ɗauki nauyin karatun 'ya'yan marigayin

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!