SABON mashawarcin Gwamnan Jihar Katsina a kan al’amuran mawaƙa, Malam Ukashat Suleiman, ya bayyana cewa ƙofar sa a buɗe ta ke a ko yaushe ga duk mawaƙin da ke buƙatar wani taimako.
Haka kuma ya ce har yanzu ofishin sa zai riƙa sa hannu cikin al’amuran al’adun gargajiya.
Ukashat, wanda mawaƙi ne, ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim jim kaɗan bayan an naɗa shi sabon muƙamin.
Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, shi ya naɗa Ukashat, wanda aka fi sani da ‘Ajuba’, a ranar Alhamis, 3 ga Oktoba, 2019.
Takardar naɗin na ɗauke da sa-hannun Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa.
Mutane da dama sun yi ta yaɗa takardar a soshiyal midiya saboda ba a saba ganin an naɗa muƙami irin wannan ba.
To amma Fim ta yi la’akari da cewa kamar canjin muƙami ne aka yi wa Ajuba. Idan ba ku manta ba, a Fim ta watan Satumba 2018 mun kawo maku labarin yadda gwamnan ya naɗa Ajuba matsayim mai ba shi shawara kan harkokin raya al’adun gargajiya.
Bayan sake lashe zaɓen 2019 a yanzu kuma aka canza masa muƙami zuwa ɓangaren mawaƙan zamani.
A lokacin da mujallar Fim ta tuntuɓi mawaƙin don jin ta bakin sa game da muƙamin, sai ya ce: “Ina godiya ga Allah (SWT), sannan kuma ina godiya ga mai girma Gwamnan Katsina, Malam Aminu Bello Masari, wato Adalin Gwamna.
“Duk mutumin da ka ji an ce gwamna ya zaɓe shi a matsayin mai ba shi shawara, to ya na da amfanin da zai yi a ɓangaren da aka ba shi.

“A matsayi na na sabon mai taimaka wa gwamna a kan mawaƙan zamani, in-sha Allah ba iya mawaƙan zamanin zan tsaya ba, ɓangaren raya al’adun gargajiya su kwantar da hankalin su, ba wai rabuwa na yi da su ba. A ko da yaushe idan su ka tuntuɓe ni a kan wani abu da ya shafi wanda za a isar wa mai girma gwamna saƙo, zan isar da shi cikin ikon Allah.
“Don haka yanzu ƙofa a buɗe ta ke ga duk mawaƙin da ya ke da wani saƙo da zai isar a gwamnatance idan ya sanar da ni, ni kuma zan isar da saƙon sa wurin da ya dace, cikin ikon Allah.”
![]()







