SHAHARARREN jarumi kuma darakta a Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu, ya lashe matsayin Jarumin Jarumai na Gasar Finafinan Nijeriya ta nahiyar Turai na bana, wato Nollywood Europe Golden Awards (NEGA 2023), wadda aka yi a birnin Frankfurt na ƙasar Jamus.
Jarumin, wanda yanzu haka ya na can Frankfurt, ya ɗora hotunan sa a soshiyal midiya riƙe da kambun sa.
Sannan ya yi rubutu da Turanci a ƙasan hotunan, inda ya ce, “Alhamdu lillah. I just won the Best Actor Award in the Nollywood Europe Golden Awards (NEGA 2023).

“My appreciation goes to the organizers ehizoyagolden, my fans across the globe, the producers, directors and colleagues that have been there for me throughout the journey. We move!”
Mujallar Fim ta fassara rubutun da cewa: Alhamdu lillah. Yanzu na lashe gwarzon Jarumin Jarumai na Nollywood Europe Golden Awards (NEGA 2023).
“Ina miƙa godiya ta ga mashiryin gasar, wato Ehizoya Golden, da masoya na a faɗin duniya, furodusoshi, daraktoci da abokan aiki na da su ka kasance tare da ni tsawon wannan tafiya. Mu je zuwa!”

Ali Nuhu ya ɗauki tsawon shekaru ya na lashe wannan matsayin a ƙasashen waje, wanda ya sa ake yi masa laƙabi da ‘Multiple Award Winning Actor’, domin babu wanda ya kai shi karɓar kambun jarumin jarumai a cikin ‘yan Kannywood a gida da wajen Nijeriya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa wannan dalilin ya na daga cikin abubuwan da su ka sa ake kiran shi da Sarkin Kannywood.


