ALI Nuhu ya bayyana yadda zai aiwatar da aikin da Skyline University of Nigeria ta ba shi a matsayin jakaden ta a Nijeriya, ya ce da ma shi mutum ne mai son ganin cigaban ilimi a ƙasar nan.
Shahararren jarumin, wanda ake yi wa laƙabi da Sarkin Kannywood, ya na magana ne a wurin naɗin da aka yi masa a hedikwatar jami’ar da ke Titin Zariya a Kano a yau Alhamis, 19 ga Agusta, 2021.
Wakilin mujallar Fim, wanda ya halarci taron, ya ruwaito cewa jami’ar ta ba Ali kwangilar jakadancin ne a ƙoƙarin ta na ganin cewa ta yi haɗin gwiwa tsakanin ta da sanannun mutane domin haɓaka harkar ilimi a Nijeriya da kuma sunan jami’ar don samun ƙarin ɗalibai.
Da ya ke jawabi jim kaɗan bayan ya rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar sa da jami’ar, Ali ya bayyana wannan naɗi da aka yi masa a matsayin wani cigaba kuma abin alfahari a gare shi.
Ya ce, “Ni wani mutum ne da yawanci ina so in ga ana ƙoƙarin taimakon na ƙasa don su ma su tsaya da ƙafar su. Kuma shi ilimi wani abu ne da ake da buƙatar sa sosai ko a addinance, domin ya na da amfani matuƙa.
“Wannan dama da na samu zan yi ƙoƙari na ga cewa manufofin jami’ar na alheri zan yaɗa su na farko kenan.

“Baya ga haka, ɗaliban da ke makarantar akwai hanyoyi da yawa da za su buƙaci mu zo a yi abubuwa tare na cigaba a harkar su ta neman ilimi da su ke yi. In-sha Allahu duk irin wannan zan yi ƙoƙari na ga cewa na yi.”
Bayan kammala taron, mujallar Fim ta tambayi Ali Nuhu yadda zai haɗa harkar fim da jakadancin wasu kamfanoni da ya ke yi. Sai ya amsa da cewa: “Kusan kowanne abu da na ke riƙe da shi za ka ga cewa ya na da nashi muhallin daban. Saboda haka kowanne zai zauna a muhallin da ya ke, kuma wannan ɗin da na ke ba zai canza wasu abubuwan da na ke yi ba. Haka kuma su ma waɗancan ba za su canza wannan ɗin da na ke yi ba.
“Kawai dai abu ɗaya da na sani shi ne abu biyu ko kuma in ce masana’antu biyu da su ke abu iri ɗaya, ba za ka iya zama jakaden su lokaci ɗaya ba; dole ɗaya za ka riƙe. Tunda a nan Allah ya ajiye ni, a nan zan zauna.”

Tun da fari da ya ke jawabi a madadin makarantar, Mataimakin Shugaban jami’ar, Mista Ajith Kumar, ya ce nagarta da jajircewar Ali ne su ka sanya su ka zaɓe shi ya zama jakaden su.
Ya ƙara da cewa su na fatan jarumin zai ba su cikakken haɗin kai wajen gudanar da al’amarin makarantar.
Taron ya samu halartar manyan jagororin makarantar da su ka haɗa da magatakarda da daraktan gudanarwa da kuma darakta mai kula da walwalar ɗalibai.
A ƙarshen taron, makarantar ta bai wa jarumin kyautar lambar karramawa.
Mujallar Fim ba ta gano yawan kuɗin da jami’ar ta yi jinga da Ali za ta biya shi ba.
Ita dai jami’ar Skyline, an kafa ta ne a cikin 2018, kuma ta na daga cikin jami’o’i masu zaman kan su a Nijeriya.

