• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Baƙin ƙabilu ne ke ɓata mana Kannywood, su na siyasantar da ita – Rashida Maisa’a

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 4, 2022
in Labarai
0
Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa'a)

Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa'a)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

RASHIDA Adamu Abdullahi (Maisa’a), Mataimakiyar Shugaba ta Ƙasa kuma ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa (Arewa Film Makers Association of Nigeria), ta bayyana cewa zaɓen ƙungiyar da aka gudanar a jiya Asabar, 3 ga Disamba, 2022 an yi shi ne ba bisa ƙa’ida ba.

Hajiya Rashida, wadda sananniyar jaruma ce, ta ce kawai dai wasu ne su ka shirya domin yin amfani da sunan ƙungiyar saboda wata manufa ta siyasa.

A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, Rashida ta yi zazzafan martani inda ta  ce wasu baƙin ƙabilu sun shigo Kannywood su na siyasantar da ita domin biyan buƙatar kan su.

Ta ce ko kaɗan ba za ta lamunta ba da zaɓen ƙungiyar furodusoshin, ta ce, “A matsayi na na ‘yar kwamitin amintattu ta ƙungiyar ‘Arewa Film Makers’ kuma ni ce mace kaɗai a ciki, kuma ni ce mataimakiyar shugaba ta ƙasa wadda aka zaɓa watanni shida da su ka wuce, to na ji wasu abubuwa a na cewa wai ana zaɓe.

“To, ina tunanin wannan zaɓen kamar ka ci tsire ne ka jefar da takardar, to haka ya. Wannan zaɓen nasu duk shirme ne. 

“Kuma kamar waɗanda su ka ɗebo su su na ganin su sun ɗebo su sun zuba su, wai a kan ba za mu iya yin magana ko ba za mu ce komai ba, 

to ai waɗanda su ka ɗebo su ka saka ba su ma isa ba ballantana. 

“Kuma ina sanar da cewa a matsayi na na mataimakiyar shugaba ta ƙasa, da zaɓen su da wasan yara duk ɗaya ne. 

“Saboda tsarin mulki ba hauka ba ne, don akwai shi mu na da shi. Kuma ba su isa su je su yi wani tsarin mulkin na gaban kan su ba. 

“Don haka duk wanda ya yi zaɓe aka ce wai an ba shi shaidar ya ci zaɓe na ƙungiyar Arewa Film Makers, to ya karɓi takardar tsire tunda shugaban ƙungiyar Arewa Film Makers na ƙasa bai saka hannu ba, sakataren sa bai saka hannu ba, don haka waɗanda su ka je su ka yi abin su. 

“Domin kullum masana’antar nan so ake a kawo rashin cigaba, wasu ‘yan jagaliya, wasu ‘yan baranda masu da su ka bayar da harkar su je nan su tsugunna kamar almajirai, su tafi nan su je su yi bara, su je nan su yi maula. 

“To ƙungiyar nan ba a isa a ce za a yi maula ko a siyasantar da ita ba, tunda ba a tsiri yin zaɓen ba sai da aka ga siyasa ta zo, wasu maƙaryata ‘yan ƙarya, waɗanda su kawai burin su kullum su ce su ne.

 “‘Yan ƙarya, to ba za a yi mana ƙarya da ‘Arewa Film Makers’ ba, sai dai su yi iyakacin ƙaryar su da su ka saba. Amma maganar Arewa, zaɓe ba a yi ba. 

“Kuma ni Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a na ke faɗa kuma sai mun ɗauki tsattsauran mataki a kan wannan shirmen da su ke ƙoƙarin su yi mana.

“Kuma za mu yi kira da jan hankali ga hukumomi a kan da su zo su duba wannan lamarin, domin zaɓen Arewa wancan da aka yi shi, ba kai-tsaye aka yi shi kamar wasa ba, sai da mu ka kirawo jami’an tsaro kowa ya sani, gwamnati ta sani, har da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ya na cikin mutanen da su ka zo wajen aka gabatar da shi a gaban sa. To kuma shi wannan ɗin fa?

“Saboda haka, ina kira ga mutane su sani wannan zaɓe shirme aka yi. Kada kowa ya damu, duk wani da ya ke riƙe da wani muƙami a ƙungiyar Arewa reshen Jihar Kano shi mu ka sani. Wannan kawai su na so su yi amfani da wannan damar su je gaban ‘yan siyasa su rinƙa ƙarya; da man su maƙaryata ne. 

“Duk waɗanda su ka yi zaɓen mun riga mun san ko su su waye su, kuma mun san me za su yi. To don haka waɗanda su ke kan muƙaman su mu na ba su haƙuri, kada su ɗaga hankalin su, su su ke da garanti, su mu ka zuba, su ne zaɓaɓɓu, su mu ka rantsar, don haka su kwantar da hankalin su.

“Mu na fatan Allah ya kawo mana zaman lafiya a masana’antar Kannywood. Duk wani da ba ya son zaman lafiya, da baƙi da su ka zo, ƙabilu su ka zo su ka cika masana’antar, su ke so su tayar mana da husuma, Ubangiji Allah ya mayar da kowa garin su, a bar mu a Jihar Kano mu zauna lafiya. 

“Kowa ya koma garin su ya zauna in ya so ya yi fim ɗin a can. Mu baƙi ba za su zo garin mu su ɓata mana harka ba. 

“Saboda gara mu fito mu fara magana a kan baƙi a masana’antar fim.”

Masu lura da harkokin industiri za su ce wannan magana da Rashida ta yi, da wuya in ba da Mansurah Isah ta ke ba, wadda sun jima ba su ɗasawa.

Idan kun tuna, a labarin da mujallar Fim ta kawo jiya, mun sanar da ku cewa Mansurar ce aka zaɓa a matsayin mataimakiyar shugabar ƙungiyar ta Arewa, reshen Jihar Kano.

Loading

Tags: AFMANArewa filmmakersKannywoodKanoƙabiluMansurah IsahRashida Adamu Abdullahi (Maisa'a)taƙaddama
Previous Post

INEC da Hukumar Sadarwa za su magance matsalar da ka iya tasowa yayin aika sakamakon zaɓen 2023 ta hanyar BVAS

Next Post

Wata 3 da rabi bayan rasuwar matar sa, furodusa Magaji Sulson ya yi rashin babban ɗan ta Mubarak a Kogin Kaduna

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Marigayi Mubarak Yahaya (a dama) da mahaifin sa, Alh. Magaji Sulaiman

Wata 3 da rabi bayan rasuwar matar sa, furodusa Magaji Sulson ya yi rashin babban ɗan ta Mubarak a Kogin Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!