MAWAƘIN yabon Manzon Allah (s.a.w.) wanda kuma ya ke yagar rabon sa a waƙoƙin siyasa, Tijjani Gandu, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya yi wa waƙa sai ɗan Kwankwasiyya, musamman a Kano.
Ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim.
A yayin da ya ke magana kan waƙoƙin siyasa, Malam Tijjani ya ce: “Ai kowa ya sani, babu wata waƙa da aka san ni da ita sai waƙar ‘Abba Gida-Gida Abba’, waƙar da ta yi tashe a zaɓen 2019 da ya gabata, kuma ina alfahari da ita don waƙa ce da ta ɗaga daraja ta a duniya.
“Kuma ni da man a siyasa ni mawaƙin Kwankwasiyya ne. In dai a Kano ne, babu wani ɗan siyasa da zan yi wa waƙa sai ɗan Kwankwasiyya da ‘yan cikin ta. Kamar yadda ka ji mu na cewa, ba mu fara don mu daina ba!”
Wani abu shi ne ba kowa ba ne ya san yadda Tijjani ya shiga harkar waƙa, amma ya faɗa a hirar sa da wakilin mu, ya ce shi kan shi bai yi zaton zai zama mawaƙi ba.
Ya ce: “Ban taɓa zaton zan zama mawaƙi ba. Kawai dai alaƙa ta da mawaƙa wadda a lokacin harkar sana’a ta a cikin su ta ke, to sai Allah ya sa na zama mawaƙi.
“Saboda a tasowa ta na yi ƙananan sana’o’i, daga ciki har da zane-zane, kuma wannan sai ya sa na ƙulla alaƙa da mawaƙa.”
Da ya ke bayani kan yadda ya rikiɗe ya zama mawaƙi, Tijjani ya ce: “Duk wanda ya ke so a yi masa zane a situdiyo ɗin sa, sai ya kira ni na yi masa. To sai ya zama na shahara a cikin su, mun saba, ina zuwa na shiga kowane situdiyo na zauna har na fara koyon kiɗa.”
Ya ci gaba da cewa, “Da yake ina yin waƙoƙi na Mauludi a makarantar mu, sai ya zama na iya rubutun waƙoƙin yabon Manzon Allah da kuma na faɗakarwa. To sai na fara da na yabon Manzon Allah. Ina yi har aka fara sani na a cikin mawaƙa.”
Ya yi waƙoƙi da yawa, amma an ɗan jima ba a san shi ba. A cewar sa, waƙar da ta fito da shi aka san shi ita ce ”Yar Maye’. “Ita ce ta sa aka san ni a duniya,” inji shi.
Mawaƙin ya yi wani kira ga abokan sana’ar sa, ya ce, “Ina kira ga mawaƙa da mu riƙe mutuncin sana’ar mu, mu kare duk wani abu da zai zubar mana da mutunci.”
Da fatan sun ji.
![]()







