• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Babu tsari a harkar saka finafinan Kannywood a YouTube, cewar Umar UK

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
October 26, 2022
in Labarai
0
Alh. Umar Sani Lawan Ƙofar Mazugal (Umar UK)

Alh. Umar Sani Lawan Ƙofar Mazugal (Umar UK)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa babu kyakkyawan tsari a yadda ‘yan Kannywood su ke harkar saka finafinan su a YouTube yanzu.

Babban furodusan nan Alhaji Umar Sani Lawan Ƙofar Mazugal, wanda aka fi sani da Umar U.K., shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim.

Umar ya ce harkar kasuwancin fim wata aba ce da ta ke karɓar duk wani cigaba da zamani ya zo da shi, to amma ya na so a yi komai a bisa tsarin da ya dace.

Furodusan, wanda ya ce babu wanda ya kai shi yawan shirya fim a masana’antar, ya ba mu labarin gwagwarmayar da ya sha kafin ya kai ƙololuwar bunƙasa a harkar shirya finafinai, ya ce: “Tun farkon shigowa ta ban ɗauki abin da wasa ba, duk da na shigo ta ne ba tare da ina da jari nawa na kai na ba, don haka sai na fara tallar sidi, da haka har na zo ina raba kaya a kasuwa, wanda kuma daga baya na zo ina turawa wasu garuruwan. 

“Kuma da yake ina da wata manufa da na zo da ita ta neman cigaba, sai na yi ƙoƙarin samun yadda zan yi na fara furodusin, kuma na fara ɗin a daidai lokacin da harkar fim ɗin ta yi zafi, lokacin Malam Rabo. Na ɗauki waƙar Nazifi Asnanic ta ‘Gari Ya Yi Zafi’ na mayar da ita fim. 

“Kuma alhamdullah, kusan zan iya cewa wannan fim ɗin shi ne sanadin ɗaukaka ta a harkar furodusin, saboda a yanzu zan iya cewa duk a masana’antar Kannywood babu wanda ya fi ni yawan furodusin ɗin fim.”

Dangane da canzawar da zamani ya yi, kuma ya bi zamanin, Umar ya ce: “Tun daga lokacin da kasuwancin sidi ya mutu, ni ma sai na sauya tsari don ganin an cigaba da damawa da ni. Don haka sai na tafi na yi karatu, inda na yi diploma a kan harkar fim. Kuma daga nan sai na ci gaba da faɗaɗa kasuwanci na inda na samar da wani situdiyo a cikin ginin ARTV wanda na ke gudanar da shirye-shirye da su ka shafi siyasa, addini, kasuwanci. Kuma a yanzu ina tabbatar maka da cewa a duk Kano babu wani situdiyo da ya ke gudanar da aiki kamar nawa. 

“Akwai wani gidan talbijin na Ghana, Gaskiya TV, to kusan mafi yawan shirye-shirye da ake ɗaukar musu, kashi 90 cikin 100 mu ne mu ke yin aikin, saboda irin kayan aikin da mu ke da shi.”

A game da yayin da ake yi na ɗora fim a YouTube, shugaban na kamfanin UK Entertainment ya ce: “Wannan abu ne mai kyau, sai dai rashin tsari ya mayar da abin baya. Domin da su masu yin harkar za su haɗe su yi harkar a channel masu ƙarfi guda biyu ko uku, to da sai sun fi cin gajiyar abin. Amma yawan buɗewa da ake yi, kowa ya buɗe nasa, sai ya zama duk abin babu tsarin da za a ci ribar abin da yawa; idan sun fara sai su daina saboda babu kuɗin da za a gudanar da shi. 

“Amma da an haɗa ƙarfi waje ɗaya, da an samu kuɗi sosai a harkar YouTube.”

Umar ya yi kira ga ‘yan Kannywood, ya ce, “Ina kira ga abokan sana’ar mu da su karɓi zamani ta hanyar tafiya da duk wani cigaba da ya zo da shi, saboda a samu a gudanar da harkar cikin tsari.”

Loading

Tags: ARTVfurodusaGaskiya TVKanokasuwanciMalam RaboNazifi Asnanicshirya fimUK EntertainmentUmar UKYouTube
Previous Post

Zaɓen 2023: Ala ya sha alwashin kare mutuncin Rarara bakin rai bakin fama

Next Post

Ambaliya: Kayan agaji sun isa jihohi 21 – Minista

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Ma'aikatan agajin gaggawa sun kai kaya a wani gari da ambaliya ta shafa

Ambaliya: Kayan agaji sun isa jihohi 21 - Minista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!