MAWAƘI a Kannywood kuma ɗan takarar zama ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (ALA), ya bayyana cewa yaƙin kare mutuncin abokin sana’ar sa kuma aminin sa mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya fi masa yaƙin neman zaɓen takarar da ya ke yi.
Ala ya yi wannan iƙirari ne a wani rubutu da ya yi a Fezbuk a yau Talata, inda ya ce, “Yaƙin kare mutuncin Dauda ya fi yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ɗan Majalisar Tarayya a gare ni.
“Mu yi mutunci da mutuncin ka, ka yi mutunci da mutuncin mu shi ne babban arziƙi na zaman tare.
“Takara ta fansa ce a wajen kare mutunci da haƙƙin Dauda.”

Sha’irin ya yi wannan rubutun tare da ɗora hoton Rarara da rubutu a jikin sa da cewa, “Yaƙin da ya cinye Doma, bai zai ƙyale Awai ba.”
Tun da farko kafin wancan rubutun, sai da Ala ya ɗora wani hoto na Rarara a Fezbuk ɗin, mai ɗauke da rubutu kamar haka: “Mugun madambaci shagon guramaɗa. Da yawa masu faɗa da kai ba su san abokin faɗan ba. Haƙiƙa da sun sani, da ba su yarda sun gwada wa kurciya baka ba.”
A saman hoton kuma sai ya rubuta, “Kallo ya koma sama ga dukkan alamu.”
Waɗannan rubuce-rubucen sun ta da ƙura, inda wasu daga cikin masu yi masa martani ke goyon bayan sa, wasu kuma na mai da masa da magana marasa daɗi.
Duk wannan ya biyo bayan turka-turkar da ke faruwa ne a masana’antar Kannywood da wasu jami’an gwamnati a Jihar Kano, inda wasu ke murna a kan cire sunan Rarara daga cikin kwamitin kamfen na ɗan takarar zama shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wasu kuma ke faɗa da shi.
![]()







