FITACCEN jarumin Kannywood Shehu Hassan Kano ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai ya makance.
Wakilin mujallar Fim ya kai masa ziyara a gidan sa da ke unguwar Fagge cikin birnin Kano, don bin bahasin maganar.
Alhaji Shehu ya faɗa masa cewa, “A kwanakin baya na yi rashin lafiya wacce ta kai ga an yi mani aikin ido.
“Ba wai makancewa na yi ba, kuma ko a yanzu haka ina ganin komai rangaɗaɗau da idanuwa na kamar yadda na ke kallon ka yanzu haka a gaba na, har ma ina iya karantu da rubutu ba matsala.”
A ‘yan kwanakin nan an yi ta yaɗa ji-ta-ji-tar cewa jarumin ya samu matsalar ido, kuma wai ba ya gani sosai.
Amma dai Shehu Kano, wanda ake wa laƙabi da Tindirƙi, ya ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba ma zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa kamar yadda ya saba.