SADIYA Abdulƙadir (Sareena) ta na ɗaya daga cikin matasan jarumai mata da ake yi wa kyakkyawar fata a cikin wannan masana’anta ta Kannywood saboda irin ƙudirin da ta ke ɗauke da shi a zuciyar ta.
A cikin wata hirar musamman da ta yi da mujallar Fim, Sareena, wadda yarinya ce mai ƙarancin shekaru, ta bayyana dalilin da ya sa ta shigo industiri tare da burin da ta ke son cimmawa kafin ta daina harkar fim.
Game da batun aure kuwa, jarumar ta faɗi irin mijin da ta ke da muradin ta aura. Ga yadda tattaunawar jarumar da wakilin mujallar Fim ta kasance:
FIM: Za mu so jin tarihin ki a taƙaice.
SADIYA SAREENA: Sareena dai haifaffiyar Azare ce da ke Jihar Bauchi. Sannan na yi makarantar firamare da sakandire duk a can garin na Azare, wanda daga nan kuma na shiga industiri.
FIM: Ke Bahaushiya ce?
SADIYA SAREENA: Ni Bafulatana ce.
FIM: A matsayin ki na matashiya kuma mai ƙananan shekaru, me ya ba ki sha’awa har ki ka shigo wannan masan’anta ta Kannywood?
SADIYA SAREENA (dariya): To ai ita harkar fim faɗakarwa ce da ma. To na tashi da burin yin fim tun ina yarinya kuma abin da ya ban sha’awa shi ne ina so in ga yau ina faɗakarwa kuma ka san yanzu mutane idan ka fito ka ce za ka musu wa’azi ba za su taɓa fahimtar ka ba, amma idan ka fito ta wata sigar kamar fim akwai nishaɗantarwa a ciki sannan akwai faɗakarwa. To wannan dalilin ne ya sa na shiga harkar fim.
FIM: Lokacin da ki ka je wa da iyayen ki da wannan maganar, me su ka ce?
SADIYA SAREENA: Gaskiya na samu tsaiko sosai, saboda akwai wani lokaci da na je gida na samu maman mu na ce mata ina so zan shiga fim, sai ta ce kar in ƙara wannan zancen. To daga baya kuma har ta zo irin ta fara yarda; ka san uwa ko yaya ita ta na bin bayan ‘yar ta ne. Amma kuma ‘yan’uwan ta maza na sha wahala kafin su yarda.
FIM: A garin ku na Azare ki ka fara fim ko sai da ki ka zo nan Kano?
SADIYA SAREENA: A’a, ban fara fim ba sai da na zo nan Kano.
FIM: Ki na da ‘yan’uwa ne a Kano ko kawai kin zo ne ki yi fim ba tare da kin san kowa ba?
SADIYA SAREENA: Ina da ‘yan’uwa a Kano, sannan kuma mu ka zo da wani yaya na na sauka a gidan ‘yan’uwa na; don maganar da na ke maka ma a can na ke da zama. Da mu ka zo da ɗan’uwan nawa sai ya ɗauke ni ya kai ni wani ofishin da ake yin fim mai suna Sirrinsu Media. Kusan zan iya ce maka shi ne ofishin fim da na ke na farko kuma na ke ciki tun bayan zuwa na Kano.

FIM: Tun bayan lokacin da ki ka zama jaruma, ko akwai wani abu da jarumi ko darakta ya yi maki wanda ba za ki taɓa mantawa da shi ba?
SADIYA SAREENA: E to, ka san abin yanzu aka fara tafiyar, dole sai ka fuskanci ƙalubale a rayuwa, musamman a ce wurin da za a taru a zauna a ce wurin aiki dole sai an samu wanda ba ku samu fuskantar juna ba tsakanin ku. Haka irin wannan ma ka ga ƙalubale ne a ciki.
Akwai kuma waɗanda idan su ka gan ka an zo an ɗauko ki, ke ba ki daɗe da zuwa ba an kuma ba ki wani babban matsayi a fim, su su na zaune ba a ba su ba, za ka ga hassada ta shiga cikin lamarin; shi ma kuma wani ƙalubale ne.
FIM: Zuwa yanzu finafinan ki nawa?
SADIYA SAREENA: E to, ba su dai da wani yawa domin uku ne kawai, waɗanda su ka haɗa da ‘Sirrin Ɓoye’ na tashar Arewa24 da ‘Macen Sirri’ da kuma wani mai suna ‘Ilimin So’.
FIM: Me ya fi burge ki a cikin wannan masana’anta?
SADIYA SAREENA: Abin da ya fi burge ni bai wuce yadda na ga ana da haɗin kai tsakanin mu da ‘yan’uwa na waɗanda mu ke zama a ofishin mu ba da yadda mu ke damuwa da damuwar ɗayan mu. To wannan abin ya na burge ni sosai.
FIM: Bayan finafinai da ki ke yi ki na da sha’awar yin wani abu?
SADIYA SAREENA: Ina son zama ‘yar kasuwa sosai da sosai.
FIM: Kin taɓa yin aure ne?
SADIYA SAREENA (dariya): To ni dai ban taɓa yin aure ba, sai dai mu na sa ran nan gaba za mu yi.
FIM: Ki na da muradin irin mijin da ki ke so ki aura?
SADIYA SAREENA: A’a. Ka san shi aure wani abu ne wanda daga zarar kun samu fuskantar juna, ba wai ki ce talaka ki ke so ba ko kuma mai kuɗi, to ni a tsari na ma ba na son mai kuɗi sosai, saboda auren irin waɗannan babu kwanciyar hankali, amma idan zan yi aure na fi son na samu mai rufin asiri kuma arziƙin sa daidai misali wanda zan iya rayuwa da shi.
FIM: Duk da yake ba ki jima a cikin wannan masan’anta ta ba, shin ko mutane sun fara gane fuskar ki?
SADIYA SAREENA: E, domin yanzu ma mutane da kan su wani lokacin ina zaune a gida su na zuwa kawai don su gaishe ni su gan ni, wasu ma mu ɗauki hoto tare.
FIM: Sau da dama wasu daga cikin al’umma na yi wa ‘yan fim wani kallo da maganganun da ba su dace ba. Ya ki ke ji idan wani ya yi maki irin wannan kira ko magana?
SADIYA SAREENA: Ba na jin daɗi sosai saboda idan an ce wannan ‘yar fim ce za ka ga cewa wasu su na yi miki kallon rashin fahimta, za a ce wannan ai ‘yar iska ce; wani na miki kallon ke karuwa ce. Ina jin zafin wannan abin.
Amma kuma in na tuna da wani abu guda ɗaya na cewa Ubangiji na shi ya halicce ni, ya kuma san me na ke aikatawa, kuma shi ya san abin da ya ke zuciya ta, ba na damuwa tunda kai ɗan’adam ba kai za ka bada Wuta ko Aljanna ba.
FIM: Wane irin buri ki ke so ki cimmawa a wannan masana’antar?
SADIYA SAREENA (dariya): Buri na? To a yanzu dai na cika buri na na farko, wato na zama jaruma kuma na zama. To yanzu kuma ina son zama wata jaruma sananniya, amma ba ta hanyar abu mara kyau ba; ina so in zama sananniya amma ta hanyar fim ɗi na, sannan ina so na zama mashahuriyar ‘yar kasuwa da yardar Allah.
FIM: A cikin wannan masan’anta ta Kannywood waɗanne mutane ne su ke ba ki gudunmawa?
SADIYA SAREENA: To gaskiya mutum na farko shi ne Maje El-Hajeej Hotoro, maigida na kenan domin kuwa ya na iya ƙoƙarin sa a kai na da kuma duk wani ɗan ofishin mu, don ko ni ba abin da zan ce masa sai dai godiya kawai.

FIM: Ki na da wani tsokaci ko shawara da za ki ba mata matasa masu tasowa?
SADIYA SAREENA: Shawarar da zan ba su ba za ta wuce cewa kar ki ga wacce ta kai wancan matsayin ke ma ki ce ko ta halin ƙaƙa sai kin je kin kai wannan matsayin ba. A duk lokacin da ka kasance mai haƙuri, shi zai kai ki ga cin ribar duk wata nasara.
Sannan a ƙarshe ina so na tunasar da masoya na da masu bibiya ta da cewa ku saka ‘yan’uwan mu da ke cikin tsaka-mai-wuya a cikin addu’o’in ku, duba da cewa wasu daga cikin jihohin Arewa na fama da matsanancin rashin tsaro. Shi ne na ke so na yi amfani da wannan dama wajen taya su da addu’a, Allah ya kawo musu ɗauki.
FIM: Mun gode da lokaci da aka ba mu.
SADIYA SAREENA: Ni ma na gode.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com